Shugaban Izala a Katsina ya koka kan yadda ake ɓata sunan malamai

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar izala ta ƙasa reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya koka akan yadda kafafen sadarwa na zamani ke ɓata sunan malaman addinin Musulunci.

Ya ce hakan ya saɓawa addinin Musulunci da koyarwa Manzon (SAW).

Shugaban ƙungiyar wanda ke magana da manema labarai a Katsina ya yi kira a gare su da su ji tsoron Allah kuma su tuna za su koma ga mahaliccin su inda za su amsa tambayoyi game da ɓatancin da su kayi.

Sheik Yakubu Musa ya kuma koka kan yadda wasu ɓatagarin mutane ke ɗaukan nauyin matasa domin cin mutuncin malamai a kafafen sadarwa da suma su ji tsoron Allah su kuma sani zasu yi bayanin irin cin mutuncin da suka yi a ranar lahira.

Ya buƙaci matasa da su tashi tsaye wajan neman ilimin addini da na zamani ba kuma kawai don neman aikin gwamnati kawai,ko sun zama masu kyawawan tarbiyya a cikin al’umma.

Shugaban ƙungiyar izalan ya kuma yi kira ga yan kasuwa da su ji tsoron Allah su rage farashin kayan abinci ko talaka ya sami sauƙi.

Haka suma shugabanni a matakin gwamnati da suma su kamanta gaskiya da riƙon amana da su guji taɓa kayan gwamnati”kuma Allah zai tambaye ku,ku yi bayanin kwabo ɗaya da ya salwanta” inji Sheikh Yakubu Musa

By ukarofi