Ina shirin duba yadda a ke sa ran dawowa don ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza tsakanin Isra’ila da Hamas sai kawai na matakin Isra’ila ta tabbatar da mamaye wasu sassan Gaza a matsayin shinge tsakanin sojan Isra’ila da waɗanda su ka bayyana a matsayin maƙiya. Ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya ce ko ma an kona duk wata yerjejeniya ta sulhu to sojojin Isra’ila za su cigaba da kasancewa a da’irar da su ka shata a Gaza. A yanzu haka Isra’ila na mamaye da kashi 20% na Gaza a matsayin yankin tsaro. Katz ya ce yankin zai zama yadda Isra’ila ta wafci wasu sassan Lebanon da Sham don tsaro. Isra’ila ta takura Falasɗinawa a kudancin Zirin Gaza da baiyana cewa ta kashe ɗaruruwan mayaƙan Hamas. Duk da zanga-zanga da a ke yi a cikin Isra’ila don buƙatar dakatar da yaki da zai sa Hamas ta sako kamammun Israi’ilawa hakan bai hana matsa lamba kan yaƙin ba. A tsarin su Katz takurawa Hamas ne zai sa ta sako kamammun. A bangaren Hamas na cewa duk wata yerjejeniya da ba za ta sa dakatar da yaƙi da janye sojojin Isra’ila daga Gaza ba to tarko ne kawai na cigaba da mamaye yankin. Daga watan jiya zuwa yanzu Isra’ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 1000 da daidaita asibitocin yankin inda majinyata ke halin sai yadda ta kasance tsakanin mutuwa da rayuwa. Wani ma abun takaicin shi ne Isra’ila na cewa za ta ba da dama ga duk mazaunin Gaza mai sha’awar ficewa daga yankin ya yi haka amma da samun tabbacin ƙasar da za ta amince da karɓar baƙuncin Falasɗinawan. Wannan a fili ya na nuna tsayawa don tabbatar da matsayar shugaban Amurka Donald Trump ta ƙaurar da Falasɗinawa daga ƙasar su. Kuma ga take-taken Isra’ila bisa kalaman Katz kasar na son mallake Gaza ne don watakila hakan ne kaɗai hanyar gamawa da Hamas gaba daya. Zuwa yanzu ƙasashen Larabawa na zuba ido kawai don da alamu su na takatsantsan da salon mulkin shugaba Trump wanda ka iya kawo mu su wata marsala a harkokin cikin gidan su. Furta kalmar Allah wadai da kashe-kashen da Isra’ila ke yi a Gaza ba zai taba hana gwamnatin Netanyahu kara kaimin zubar da jinin ba don ko kaɗan gwamnatin mai tsaurin ra’ayi ba ta ɗau jinin Falasɗinawa a matsayin mai daraja ba.
Saudiyya ta yi Allah wadai da harba makamai masu linzami biyu da Isra’ila ta yi kan asibitin Al-Ahli Baptist da ke Zirin Gaza.
A nan Saudiyya ta ce wannan ƙarara keta dukkannin dokokin duniya ne da ke kare asibitoci daga hare-hare.
Tun gabanin nan ma hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce harin Isra’ila kan asibitin ya yi sanadiyyar mutuwar wani yaro.
Halin da asibitin ya shiga ya sa dole ya ƙaurar da kashi 50% na majinyata zuwa wasu asibitocin amma kashi 40% da ke mawuyacin hali ba zai yiwu a iya ƙaurar da su ba.
Saudiyya ta bukaci kasashen duniya su yi amfani da haƙƙin da ke rataye a wuyan su wajen hana Isra’ila dirar miƙiya kan asibitoci.
Isra’ila kan fake da cewa ta kan aukawa asibitoci ne don zargin ‘yan Hamas na amfani da su wajen tsara hare-hare.
Direbobi masu aiki da waɗanda ke jiran maye gurbi da su ka sa hannu kan takardar buƙatar dawo da sauran fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas za su rasa aiki.
Waɗannan direbobin kimanin 1000 sun rantaba hannu kan takardar da a ka wallafa a jaridu da ke buƙatar a tsagaita yaƙi don hakan ya ba da damar dawo da fursonin cikin salama.
Direbobin na ganin dagewa kan yaƙi ba zai taimaka ba sai ma jefa rayuwar fursnonin a barazana da ma asarar rayukan sojojin Isra’ila da wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Direbobin sun ce yaƙin bai shafi tsaro ba sai dai kare muradun siyasa da na kashin kai.
Tuni Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya mara baya ga korar duk direbobin da su ka sanya hannu daga aiki.
Hamas na nazarin amincewa da tsarin tsagaita wuta na Isra’ila:
ƙungiyar Hamas mai mulkin Gaza na nazarin amincewa da tsarin da Isra’ila ta gabatar don samun tsagaita wuta a hare-hare ko yaƙin Gaza.
Wani babban jami’in Hamas ya bayyana cewa ƙungiyar za ta fitar da matsaya da kuma tura tawaga aasar ƙatar don tattaunawa ta bayan fage da Isra’ila.
Wannan na zuwa ne bayan ma’aikatar lafiyar Gaza ta tabbatar da mutuwar mutum 38 a rana ɗaya tak sanadiyyar hare-haren Isra’ila.
Hamas na tattaunawa da jagororin ta da sauran ƙungiyoyin gwagwarmaya don ɗaukar matsaya ta bai ɗaya kan sabon shirin yarjejeniyar.
Tuni wasu tawagogin Hamas na tattauna batun a birnin Alkahira na Masar da duba sako 8-10 na kamammun Isra’ila da ke hannun ta amma da duba ko hakan zai kawo dakatar da yaƙin gaba daya.
Tattaunawar a Doha na Katar zai dawo a cikin ‘yan kwanakin nan bayan wargajewar yarjejeniyar ta tsawon mako 8 daga watan Janairu.
Tun akasin dakatar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a watan jiya, Isra’ila ta kashe ɗaruruwan Falasɗinawa a Gaza.
Hakanan Isra’ila ta yi amfani da ƙarfin ta marar kima wajen hana shigar da kayan agaji da a ke matuƙar buƙata a Gaza.
A gefe guda kasar Jodan ta kama mutum 16 ta na mai tuhumar su da neman kawo barazana ga tsaron kasar.
Hukumar bayanan sirri ta ƙasar ta bayyana kama mutanen da karin bayanin gano makamai har da kare makamai masu linzami da neman kera jirage marar sa matuƙi.
Hakanan Jodan ta ce tun 2021 ta na duba aiyukan ƙungiyar da a ke zargin da har ma ta tura wasu jami’an ta kasar Lebanon don samun horon yaƙi.
A nan hukumar bayanan na sirri ta ambata sunan Ibrahim Muhammed a matsayin madugun tafiyar kuma ta na shirin gurfanar da mutanen gaban kotu.
Ba ƙarin bayani kan ƙungiyar na shirin hare-hare ne don kifar da sarautar Sarki Abdullah ko kai hare-hare wasu ƙasashe.
A dai makwabta shugaban ƙasar Sham wato Siriya ya sauka a Abu Dhabi inda ya gana da shugaban Daular Larabawa Sheikh Zayed Al-Nahyan.
Shugaban na Sham Ahmed Al-Sharaa na ƙoƙarin inganta hulɗar ƙasar sa da ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Turai don cimma burin sauyin da ya ke son kawowa a ƙasar ta Larabawa.
Shugaba Daular Larabawa Sheikh Al-Nahyan ya nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin ta Damaskas da yadda ta ke inganta diflomasiyya da harkokin tsaron ƙasar.
Bayan kama mulki a watan Janairu biyo bayan faɗuwar gwamnatin Al-Assad a watan Disambar bara, Al-Sharaa ya ziyarci Saudiyya a watan Febreru a matsayin ziyararaiki ta farko tun hawa madafun iko.
Har yanzu Sham na fama da hare-hare da Isra’ila ke kai wa cikin ƙasar da sunan farautar mayaƙan Hezbollah ko sauran dakarun Iran da ke ƙasar.
Al-Sharaa na yunƙurin dakatar da keta alfarmar ƙasar daga ƙetare inda ya nemi lallai duniya ta shiga tsakani wajen dakatar da Isra’ila daga keta haddi.
Kammalawa;
Su ma Houthi da ke mara baya ga Hamas na fama da hare-haren Donald Trump. Harin da Amurka ta kai kan sassan Yaman da ke hannun Houthi ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 3.
Wannan harin ya biyo bayan hari a yankin Hodeida da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 13 kuma shi ne hari a lokaci daya da ya fi kowa asarar rayuka.
Houthi ta ce akasarin waɗanda harin ya shafa mata ne da ƙananan yara inda kuma a ka samu mutum 15 sun samu raunuka.
ƙungiyarta Houthi da ke samun goyon bayan Iran kuma ta ke marawa Hamas baya ta nuna hoton wani jirgi marar matuƙi da ta ce na Amurka ne ta harbo.
Tun fara hare-haren na Amurka kan Houthi don hana ta cilla makamai kan jiragen ruwan ƙasashe masu marawa Isra’ila baya a yaƙin Gaza, sama da mutum 100 sun rasa ran su
Don haka kar a yi mamakin yadda ƙasashen Larabawa ke yin kadaran-kadahan kan yaƙin Gaza.
