An yi kira ga gwamnatin Katsina ta duba lamarin yara ƙanana masu barace-barace

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Malami a jami’ar gwamnatin tarayya FUDMA da ke Dutsinma a Jihar Katsina Farfesa Aliyu Ƙanƙara yayi wannan kira a Katsina lokacin da yake hira da manema labarai.

Ya ce waɗannan ƙananan yara da akasarin su yan shekara ƙasa da biyar, ba ma barace barace ba harma da kwana a kan manyan titunan jihar.

Farfesa Ƙankara ya bada labarin wani ƙaramin yaro da ya bashi tausayi da ya ganshi a tashar sufuri ta KSTA a Katsina ya na zaune wanda ya bashi tausayi har ya yi ƙoƙarin tallafawa yaron da abinci,magani da wajen kwana ganin dare yayi a lokacin.

Ya bayyana cewa wasu mazauna garin sun shaida masa cewa sun sha maida taron wajen iyayen sa a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa amma daga baya ya gudu.

Domin haka malamin jami’ar ya yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ɗauki mataki na gaggawa ga irin wannan matsalolin da suka fara zama ruwan dare a babban birnin yace .

Ƙanƙara ya jawo hankalin gwamnatin jihar kan halin yanayin tsaro da ake fama dashi,”kada wasu ɓatagari su yi amfani da waɗannan yara wajen dagula harkokin tsaro a jihar.

Ya ce ana danganta matsalar barace-barace da halin ƙuncin rayuwar da ake fama da shi,wasu kuma suke yawan haihuwa barkatai ba tare da tanadi na kulawa da yaran ba.

Domin haka idan gwamnati bata ɗauki mataki ba, yana iya zama barazana ga tsaron a jihar.

By ukarofi