Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Hon. Bilyaminu Moriki ya bayyana warewar da wasu ‘yan majalisa su goma suka yi cewar sun kafa tasu majilisar dokokin a jihar a matsayin mara tushe da rashin bin tsarin dimukraɗiyya.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ofishinsa ranar Alhamis a harabar majalisar dokokin jihar da ke Gusau.
A cewarsa, majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancinsa tana nan daram kuma halastacciyar majalisa ce a jihar.
“Kamar yadda muka sani, muna da halaltacciyar majalisa guda ɗaya kawai a jihar Zamfara, kuma mun ɗauki taron nasu a matsayin maras tushe balle makama,” inji shi.
Shugaban majalisar ya bayyana cewa a halin yanzu shari’arsu tana gaban kotu, yana mai cewa matakin da ‘yan majalisar suka ɗauka ya saɓa wa shari’a kuma raini ne ga umarnin kotu.
“Ba mu da wani abu da za mu yi akan matakin da suka ɗauka saboda muna bin umarnin kotu,” ya ƙara da cewa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su kwantar da hankulansu kuma su kasance masu bin doka da oda, inda ya yi nuni da cewa majalisar dokokin jihar da ke ƙarƙashinsa ta himmatu wajen ci gaban jihar.
