Ribadu ya bai wa Benuwai tabbacin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mai ba wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan tsaro (NSA) Mallam Nuhu Ribadu, a ranar Talata ya ba wa mutanen jihar Benuwai tabbacin cewa gwamnatin tarayya na duk mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Ribadu ya ba da wannan tabbaci ne a lokacin wani taro na masu ruwa da tsaki a Makurdi, biyo bayan kisan mutane 72 a ƙaramar hukumar Ukum da Logo a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya jaddada cewa ba jihar Benuwai ce kawai ke fama da matsalar tsaro ba yana mai cewa ƙasar bakiɗaya na fama da wannan matsala.

Sannan ya bayyana kisan da mummunan ibtila’i kuma gwamnatin Tinubu ta gaji ƙasa wacce ke cike da rikice-rikice, amma tana aiki domin magance wannan matsala.

“Na zo nan ne domin na taya ku alhinin da kafatannin mutanen jihar Benuwai kan wannan rashi da aka yi da ba ku tabbacin muna tare da ku.”

“Shugaban ƙasa yana tare da ku a wannan lokaci mai matuƙar wahala.”

“Wannan lokaci ne na baƙin ciki kuma a irin lokacin ne kake gane masoyanka.”

“Abin da ya faru ibtila’i ne – aikin marasa imani ne, amma idan irin wannan ta zo, al’umma ce za ta haɗa kai ta tunkare ta.”

“Benue jiha ce mai matuƙar muhimmanci a Nijeriya. Cibiyar samar da abinci ce ga ƙasar nan

Ku ne na ɗaya wajen samar da abinci, kuma muna alfahari da ku.

“Za mu warware wannan matsala tare. Ka da ku je kamar ku kaɗai ne – wannan abu ne da ya shafe mu bakiɗaya.

“Dakarunmu da sauran jami’an tsaro suna iya bakin ƙoƙarinsu, duk da cewa irin wannan abu na cigaba da faruwa sakamakon abu ne mai wahala iya tura jami’an tsaro kowanne ƙauye.

“ƙasashe na samun kansu a cikin mawuyacin halli. Matsalar tsaro babban ƙalubale ne.”

“Cutar da mutane abu ne mai sauƙi, amma magance shi babban abu ne mai wuya, amma duk da haka, muna iya bakin ƙoƙarinmu.

“A matsayinmu na gwamnati wacce ba ta wuce shekaru biyu da kafuwa, mun yi nasarar rage tashe-tashen hankula da muka gada,” inji Ribadu.

Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jihar, Hyacinth Alia ya bayyana lamarin da na alhini yana mai cewa jihar an daɗe ana kawo mata farmaki da rasa rayuka tun 2011.

Ya koka game da kisan da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga suke yi wanda yake shafar tattalin arziƙin Nijeriya.

“Waɗannan mutane ba wani dalili na rayuwa cikin al’umma mai son zaman lafiya. Mun yi asarar rayuka da ta gonaki da kadarori.

“Akwai sansanonin ‘yan gudun hijira a ƙalla 17 a jihar nan, kuma har yanzu wasu sun kasa koma gidajensu.

“Sankera ita ce cibiyar samar da abinci a jihar nan, amma har ita ana ta kai mata hare-hare ba ƙaƙƙautawa.

“A maimakon murnar kyakkyawar Juma’a, abin da muka gani ita ce baƙar Juma’a sakamakon hare-haren da aka kai kan mutanen Katsina-Ala da Ukum da Logo.

“Jami’an tsaronmu suna ta aiki ba ji, ba gani, amma ina kuma muna buƙatar tallafi.

“Shugaban ƙasa yana tallafa mana kuma muna sa ran a yanzu ma zai tallafa mana,” inji gwamnan.

By ukarofi