Ranar Littafi ta Duniya: An yi kira da a farfaɗo da al’adar karatu a cikin al’umma

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A yayin da ake bikin ranar Littafi ta duniya, an buƙaci ɗalibai a matakai daban-daban na ilimi a Nijeriya da su farfaɗo da muhimmiyar al’adar karatu, duba da irin rawar da littattafai ke takawa wajen samar da ci gaban ƙasa.

Wannan kira ya fito ne daga bakin Mal. Yunusa Zakaria Ya’u, babban mai ba da shawara na Kamfanin Fombina Imprints Limited, a lokacin wani taron bitar da aka gudanar a Jami’ar Isyaka Rabi’u (Khairun) da ke Kano, ranar Alhamis.

Taken ranar shi ne : “Rashin daidaito na raguwar al’adar Karatu, da ƙalubalen wallafa a zamanin Fasaha: Matsayin littattafai wajen dawo da inganci da sauyi a fannin ilimi.”

Zakari Ya’u da ya samu wakilci Malam Isa Garba, Ya’u ya jaddada irin tasirin da adabi ke da shi wajen gina ɗabi’u a cikin al’umma, faɗaɗa hangen nesa, da kuma samar da kyakkyawan tsari na gaba. Ya ce, bikin Ranar Littafi tare da ɗalibai ba wai kawai yana farfaɗo da karatu bane, har ila yau yana ƙarfafa alaƙa mai ƙarfi tsakanin masu karatu, marubuta da kuma muhallin da suka fito

“Muna so mu farfado da wannan al’ada kuma mu duba yadda za a daraja marubuta da masu wallafa ta hanyar karanta ayyukansu, fahimtar tunaninsu, da kuma godiya da ƙarfin baiwar kalmomin da suka rubuta,” in ji shi.

A matsayinsa na mai wallafa, Ya’u ya ce irin wannan biki kamar Ranar Littafi yana da muhimmanci wajen mayar da hankalin matasa kan karatu da ilimi mai ma’ana, maimakon ƙayyadadden lokacin da suke ɓatawa a abubuwan da ba sa amfanarwa.

Sannan ya shawarci ɗalibai da su yi amfani da littattafai na zahiri da na e-copy, tare da amfani da wayoyinsu ta hanyar da ta dace. “Muna ƙarfafa matasa da su yi amfani da wayoyinsu cikin hikima—ta hanyar nemo abubuwan da ke magance matsalolin rayuwa, ba wai nishaɗi kawai ba,” Inji Yunusa Yau

Ita kuwa Farfesa Asabe Sadiya Muhammad shugabar kwalejin ilimi ta Aminu Saleh da ke Azaren jihar Bauchi, ta bayyana cewa kowace rana ma ya kamata ta zama ranar littafi ce domin littafi yana tattare da karatu da rubutu, ita kanta rayuwa ta dogara ne akan karatu, don haka rana ce mai muhimmancin gaske.

Ta ƙara da cewa “fasahar sadarwa tana nema ta ƙwace harkar karatu kwacewar kuma ba abu bane mai kyau, domin kowanne da gurbinsa ya kamata kowane a barshi ya taka rawarsa mu kuma mu tsare shi mu kare shi, domin idan muka bari harkar karatu ta lalace to fa za’a nemi rubutu a rasa, abin takaici yaran mu a yanzu sukan tashi da kalle-kalle da waƙe-waƙe ba sa iya rubutu sai ƙalilan, don haka nake kira da al’ummar mu a dawo da karatu kamar na ajami da na larabci da na boko waɗanda muka sani tun a da mu riƙe shi abubuwa masu kyau na zamani su ma mu ɗauko su mu riƙe su” inji Farfesa. Asabe

Masu jawabi a taron, ciki har da malamai da masana harkar wallafa, sun jaddada muhimmancin gina al’adar karatu da wallafa a matsayin hanya ta samun ilimi da ci gaba.

A shekara 1995 ne dai Gadauniyar raya ilimi ta majalisar ɗinkin duniya UNESCO ta ware duk ranar 23 ga watan Afrilu ta zama Ranar Littafi ta Duniya domin jaddada ƙarfin da littattafai da adabi ke da shi wajen haɗa kan mutane, ya kuma haifar da ƙirƙira, da sauyi a cikin al’umma.

Kazalika rana ce ta tunawa da rasuwar fitattun marubuta, da kuma jaddada muhimmancin haƙƙin mallakar rubutu da haƙƙin marubuta a duniya.

Taron dai ya samu halartar shugaban Jami’ar Khairun Professor da manyan malamai daga jami’o’i da marubuta irinsu Dr. Ismaila Bala da Mal. Ado Ahmad gidan Dabino da ɗalibai da sauransu.

By ukarofi