Mayaƙan RSF sun hallaka fararen hula 30 a wasu hare-hare da suka kai El-Fasher

Spread the love

Wasu hare-hare da mayaƙan RSF suka kai ta hanyar amfani da muggan makamai sun kashe fararen hula sama da 30 a garin El Fasher na Darfour.

A cewar wasu bayanai, hara-haren da aka kai a ƙarshen makon da ya gabata, sun kuma jikkata gomman mutane.

Mayaƙan RSF waɗanda wani tsagi ne na tsohuwar gwamnatin Sudan, sun shafe shekaru biyu suna tabka rikici da dakarun gwamnati ƙasar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan.

Bayan sun rasa iko da babban birnin ƙasar Khartoum a watan Maris, mayaƙan sun zafafa hare-harensu a yankin Darfour da nufin kwato garin El Fasher da bai daɗe da subulemusu ba.

A ranar 13 ga watan Afrilu mayaƙan na RSF suka sanar da kwace sansanin Zamzam da ke El Fasher, mai ƙunshe da ƴan gudun hijra sama da 500,000 yayin wasu hare-hare da suka ƙaddamar, da a cikinsu fareran hula sama da 400 suka rasa rayukansu.

Rikicin da aka shafe shekaru biyu anayinsa a Sudan, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, da tilasta wa wasu miliyan 13 barin muhallansu tare da jefa wani ƙangare na ƙasar cikin matsananciyar yunwa.

By ukarofi