Ɗaliban ajin 1982 sun sake haɗuwa bayan shekaru 43 a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Tsoffin ɗaliban shekarar karatu ta 1982 na makarantar sakandaren gwamanti ta Government Secondary School Billiri, ƙarƙashin ƙungiyar tsoffin ɗalibai ta Billiri (BILOSA), sun sake haɗuwa a wani taron tarihi bayan shafe shekaru 43, wanda ya tada tsofaffin tunane-tunane tare da ƙarfafa zumunci.

Taron ya gudana ne a Kwalejin Horas da Malamai ta Gwamantin Tarayya wato Federal College of Education (Technical) Gombe, FCE ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Malam Abubakar Abdullahi.

A jawabinsa, Malam Abdullahi ya nuna godiya bisa yawan waɗanda suka halarci taron, tare da bayyana irin ƙoƙarin da aka yi wajen sake haɗuwa da tsofaffin abokan karatu ta hanyar tuntuɓa da kuma kafa wata ƙungiya a dandalin WhatsApp.

“Manufarmu ita ce inganta haɗin kai, bayar da tallafi ga mambobi, da kuma taimakawa al’ummar ɓilliri,” inji Malam Abdullahi, yayin da ya yi kira ga sauran tsoffin ɗalibai da suka halarci taruka na gaba.

ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka haskaka taron shi ne halartar Malam Hashim, tsohon malamin Islamic Religious Knowledge, wanda ya gabatar da jawabi mai cike da nishaɗi da hikima, wanda ya ƙara nuna zurfin alaƙa tsakanin malamai da ɗalibai.

ƙungiyar ta ɗauki alƙawarin mayar da hankali kan jin daɗin mambobi, inda aka bada labarin nasarar gina gida da bayar da tallafin lafiya ga wani tsohon ɗan ajin su da ke fama da matsanancin hali.

Haka nan kuma, an tattauna kan yadda za a yi zaman ritaya mai albarka bayan kammala aikin gwamanti da wasun su suka yi, tare da maida hankali kan lafiya, kasuwanci, da kuma kula da harkokin kuɗi.

An cimma matsayar naɗa masu kula da yankuna daban-daban, farfaɗo da asusun ajiyar ƙungiyar a banki, da kuma tsara hanyoyin tallafi na mambobi.

An kuma tsara gudanar da taron na gaba a watan Disamba 2025 don ci gaba da abin da aka fara.

Wani mahalarcin taron ya bayyana muhimmancin wannan haɗuwar da cewa: “Wannan ba kawai ƙungiya ba ce; iyali ne da ke haɗe da tarihi ɗaya.”

Taron ya samu halartar mutum 94 da kuma kyakkyawan shiri na gaba, BILOSA ’82 ta kafa tushe mai ƙarfi don ci gaba da haɗin kai da taimakon juna.

By ukarofi