Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tuɓe bisa gado a cikin ɗakinsa a yakin Alo da ke ƙaramar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi.
An tsinci gawar masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata.
Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon rashin ganin matashin ya buɗe ƙofarsa da safe kamar yadda ya saba.
Daga nan ne ya sanar da ɗan uwan matashin da kuma ’yan sanda, inda suka so aka ɓalla ƙofar ɗakin, inda aka samu masoyan sun kwanta dama.
Ya ce da shigan ɗan uwan mamamcin ya tsinci gawar masoyan biyu tsirara a bisa gado bayan da aka ɓalla ƙofar ɗakin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya ce suna gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Aya ya ce, ”DPO na Ankpa na ya tura jami’an da suka je aka gano gawarwakin aka kai su asbiti a Ankpa inda aka tabbatar rai ya yi halinsa.”
