Gwamna Okpebholo ya dakatar da Basarake a Edo bisa zargin garkuwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya dakatar da Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode, a ƙaramar Hukumar Etsako East, wato George Egabor, saboda yawaitar garkuwa da mutane da kisan gillar da ake ta samu a yankinsa.

A cewar wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Fred Itua, ya sanya wa hannu, an dakatar da basaraken ne ba tare da ƙayyadadden lokaci ba saboda ƙarancin tsaro da yawaitar garkuwa da mutane da kisan kai a masarautarsa.

Sanarwar ta bayyana cewa, an kama sakataren basaraken, wato Peter Omiogbemhi, bayan wani sabon lamari da ya yi sanadin mutuwar wani daga cikin manyan fadawan fada, Marigayi John Ikhamate.

Sanarwar ta ce: “Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayar da umarnin dakatar da Dakta George Oshiapi Egabor, wanda shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode, a ƙaramar Hukumar Estako East ta Jihar Edo, saboda yawaitar garkuwa da mutane da kashe-kashe a yankinsa.

“Tuni dai aka kama sakatarensa, Cif Peter Omiogbemhi, bisa alaƙa da wani mummunan lamari da ya janyo mutuwar wani babban bafade, Marigayi John Ikhamate.

“Dakatarwar ba ta da ƙayyadadden lokaci.”

A tuna, a ranar Litinin, 3 ga Maris, 2025, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani limamin cocin Katolika, mai suna Philip Ekeli, da wani ɗalibin firistanci mai suna Peter Andrew.

An sace su ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a cocin Katolika na St. Peter da ke Iɓiukwa, kusa da Agenebode, a ƙaramar Hukumar Etsako East ta Jihar Edo.

Yayin da aka saki Limamin cocin daga hannun masu garkuwa, sai dai abin takaici, ɗalibin firistancin an kashe shi.

By ukarofi