Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin da yake ganawa da mambobin kwamitin gudanarwa kan tsarin dabarun yaƙi da ƙarancin abinci wanda shugaban ƙasa ya kafa, a fadar shugaban ƙasa.
Shirin yaƙi da tsadar abinci da bunƙasa albarkatun gona na NAPM, wani ɓangare ne na samar da daidaito a ɓangaren musayar bayanai kan harkokin noma da nufin samar da tsarin cinikayya ta bai‐ɗaya a ɓangaren albarkatun gona.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana shirin a matsayin wani abu da aka ɗauki dogon lokaci ana ƙoƙarin ƙyanƙyashewa, kuma a cewarsa yanzu ne lokacin da ya kamata a ci amfaninsa.
Idan ba a manta ba, a watan Maris din bana ne gwamnatin Najeriya da takwararta ta Brazil suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin haɗin gwiwa da ake wa lakabi da Green Imperative Project (GIP), shirin na kimanin dalar Amurka biliyan 1.1 zai farfaɗo da matsakaitan gonakin Najeriya har 774 ta hanyar amfani da fasahar noma ta ƙasar Brazil don samar da dubban ayyukan yi da bunƙasa ɓangaren samar da kayayyakin da aka ƙera a Najeriya.
Kashim Shettima ya ƙara da cewa tuni Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa wato NEMA damar kashe Naira Bilyan 15 don tunkarar barazanar ambaliya a lokacin damuna wanda ka iya kawo tsaiko ga harkokin noma da zamantakewa.
A nata jawabin, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa a ɓangaren fasahar noma, Marion Moon, ta bayyana cewa babban aikin da ke gaban NAPM Shine magance hauhawar farashin kayan masarufi da amfanin noma zuwa ƙasa da kashi 60 daga 100 na farashin Ƙasa da Ƙasa.
Marion ta ƙara da cewa tuni suka fara atisaye a jihohi 13, inda za a ƙaddamar da aikin kai tsaye a watan Yunin wannan shekarar, Kuma a bayyane yake idan aka ƙaddamar da wannan shiri zai samar da tsarin bai ɗaya a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗen jama’a da haɓaka ci gaban ƙauyuka da birane, sakamakon inganta tsarin noma da daidaita bayanai a tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
