Uwargidan gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da gangamin wayar da kai kan rigakafin kyanda

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta ƙaddamar da wayar da kan jama’a na yini ɗaya kan muhimmancin rigakafin cutar kyanda (MR) a jihar.
.
An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Garba Nadama JB Yakubu Secretariat Juma’a.

Ta ce shirin wayar da kan jama’a kan allurar rigakafin cutar kyanda zai kai ga kowa da kowa don isa ga al’umma domin tabbatar da cewa kowane yaro anyi masa rigakafin.

Hajiya Huriyya Dauda ta kuma umarci ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar da ta duƙufa wajen wayar da kan jama’a dangane da rigakafin.

A cewarta, kowane yaro daga wata 9 zuwa shekara goma sha biyar za a yi masa allurar rigakafin a faɗin jihar.

Ta ci gaba da cewa an tsara wayar da kan jama’ar ne domin tabbatar da rigakafin cutar kyanda a tsakanin yara ƙanana.

Hajiya Huriyya ta yi nuni da cewa allurar kyauta ce, inda ta ce allurar ba ta da illa.

Ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki, MDAs, cibiyoyin addini da ssarakunan gargajiya a jihar domin kare lafiyar yara a jihar.

Ta kuma buƙaci sarakunan gargajiya da malaman addini a jihar da su marawa gwamnati baya domin samun nasarar aiwatar da rigakafin a jihar.

By ukarofi