Daga JOHN D. WADA a Lafiya
A yanzu haka Honorabul Margaret Elayo ce ta zama sabuwar kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albakatun ƙasa ta gwamnatin jihar Nasarawa kuma mace ta farko da ta riƙe muƙamin a tarihin ma’aikatar kawo yanzu.
Hakan ya biyo bayan wani gyare-gyare da canje-canje na musamman ne da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule yayi wa wasu kwamishinonin gwamnatinsa a makon da ya gabata ciki har da ita Honorabul Margaret Elayo ɗin wace aka mayar da ita ma’aikatar muhallin da albarkatun ƙasa wato daga tsohuwar ma’aikatarta ta harkokin mata da ayyukan jinƙai.
A jawabinta na karɓan ragamar shugabancin sabuwar ma’aikatar nata wadda aka gudanar a babban ɗakin taro na ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa dake Lafiya babban birnin jihar a makon da ya gabata, Margaret Elayo ta bayyana canjin ma’aikatar a matsayin wani dama ce da za ta cigaba da bada gararumar gudunmawar ta wajen cigaban jihar bakiɗaya ta aiki tuƙuru kamar yadda ta saba.
Ta gode wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da damar inda ta ce ba za ta ɓata lokaci ba wajen fara ƙirƙiro tare da aiwatar da ingantattun shirye-shirye da za su inganta harkokin ma’aikatar musamman a fannin tsaftace muhalli da sauransu kana ta buƙaci duka ma’aikatan sabuwar ma’aikatar nata su bada cikakken goyon baya don samun nasara.
Har ila yau honorabul Margaret Elayo ta kuma yaba wa tsohon kwamishinan ma’aikatan Barista Isaac Dangadi wanda shi kuma aka mayar da shi ma’aikatar shari’a inda ta ce tabbas ya yi iya ƙoƙarinsa wajen canja fasalin ma’aikatar a iya ƙalilan lokaci da ya yi a wajen.
Shi ma a nasa jawabin tun farko tsohon kwamishinan ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa wanda yanzu shine sabon kwamishinan shari’a a jihar Barista Isaac ɗanladi ya bayyana Honorabul Margaret Elayo a matsayin mace mai kamar maza wace ya ce ba shakka za ta cigaba daga inda ya tsaya ta fannin aiwatar da ingantattun shirye-shirye da za su cigaba da ɗaukaka ma’aikatar kana shi ma ya yi kira na musamman ga duka ma’aikatan ma’aikatar su tabbatar suna ba ta cikakken goyon baya don ta kai ma’aikatar da jihar baki ɗaya tudun muntsira.
Sauran abubuwa da aka gudanar a wajen taron karɓar ragamar ma’aikatar daga Barista Isaac zuwa ga Honorabul Margaret Elayo sun haɗa da miƙa wa sabuwar kwamishiniyar Honorabul Margaret Elayo takardun kama aiki daga Isaac ɗanladi da ɗaukan hotuna kana suka kuma duba wasu sassan ma’aikatar daban-daban da sauransu.
