Hukumar ‘yan sandan Kano ta sanar da hanyoyin da jama’a za su kare kai daga gobara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, sfipma, mnim, mnips, masis, na sanar da jama’a game da jerin gobara da suka auku a wasu wurare daban-daban ciki har da kamfanoni, kasuwanni, gidajen zama da kuma matatun iskar gas. Haɗin gwiwar bincike da masana harkar kashe gobara ya nuna cewa hauhawar zafin yanayi da sakaci ne suka haddasa waɗannan gobara. Wannan matsala na barazana ga rayuka da dukiyar al’umma a jihar.

A dukkan lokuta, Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jiha, sun ɗauki matakin gaggawa don ceton rayuka da kare dukiya.

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano na kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan da kuma bin hanyoyin kariya don rage yiwuwar aukuwar gobara. Ga wasu daga cikin matakan da ake bada shawarar a ɗauka:

Samar da kayan kariya: Tabbatar da cewa an tanadi kayan kashe gobara a wuraren da kowa zai iya isa da su a gida, ofis, da kasuwanci.

Gyaran kayayyaki akai-akai: A duba na’urorin lantarki, wayoyi da kwalayen gas akai-akai don kauce wa haɗarin gobara.

Kashe na’urorin lantarki: A rika kashe duk wata na’ura da ba a amfani da ita, musamman da dare ko bayan fita daga ofis.

Shirya wa gobara: A tanadi tsari ko hanyar fita yayin gobara da yin atisayen ficewa lokaci-lokaci.

Bayar da rahoto: A hanzarta kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko hukumar gaggawa idan aka ga gobara ko wani abin da ake zargi.

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano na yaba wa Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jiha bisa ƙoƙarinsu na gaggawa wajen amsa kiran gaggawa na gobara kwanan nan. Wannan aiki na su ya taimaka wajen ceton rayuka da hana asarar dukiya mai yawa.

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano na ci gaba da himmatuwa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya. Muna roƙon jama’a da su kasance masu lura da muhallinsu da kuma kai rahoton duk wani abu da ka iya janyo gobara ko wani abu da ake zargi. Tare zamu iya kauce wa gobara da tabbatar da lafiyar jama’a.

By ukarofi