Easter: ‘Yan siyasa da maciya amanar ƙasa ke kitsa matsalolin tsaron da ake ciki yanzu – CAN, ACF

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja

Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya (FCT), Fasto John Joseph Hayab, ya shawarci ‘yan Nijeriya musamman masu riƙe da muƙaman gwamnati da su guji cin amanar ƙasa kamar yadda Yahuda Iskariyot ya yi wa Yesu Almasihu.

Fasto Hayab ya ce cin amana ya haifar da babbar koma baya a ci gaban Nijeriya, inda ‘yan ƙasa ke cin amanar juna da kuma da ƙasa gabaɗaya.

A cikin saƙon Easter da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna mai taken “Nasara akan Cin Amana a Easter”, ya ce: “‘Yan Nijeriya na cin amanar ƙasa da juna, shi ya sa muke fuskantar waɗannan matsaloli.”

Ya bayyana cewa hukumomin tsaro ba sa samun nasara saboda ana cin amanar ayyukansu, inda wasu ke tona asirin dabaru da shirye-shiryensu ga ‘yan ta’adda.

Ya bada misalin Littafi Mai Tsarki inda Yahuda Iskariyot ya yarda ya sayar da Yesu saboda kuɗi, sannan daga baya ya gane kuskurensa ya kashe kansa.

Ya yi gargaɗi cewa: “Cin amanar mutane – ko da mutum ɗaya ne, ko al’umma ko ƙasa – baya ƙarewa da alheri,” yana mai cewa duk wanda ke amfani da muƙaminsa wajen cin hanci ko almubazzaranci, ya ci amanar al’umma.

Ya roƙi waɗanda ke ƙoƙarin dagula ƙasa ko cutar da wasu da su daina, yana mai kira da a haɗa kai da jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.

A saƙonsu na Easter, ƙungiyar Arewa Consultatiɓe Forum (ACF) ta ce tana sane da cewa ana bikin Easter na 2025 ne a cikin mawuyacin hali na matsalolin tattalin arziki, siyasa da tsaro.

A wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Tukur Muhammad Baba ya fitar a ranar Lahadi, ACF ta nuna damuwa kan kashe-kashen da ke faruwa a jihohin Benue, Borno, Abuja, Katsina, Kaduna, Neja, Filato da Zamfara.

ACF ta buƙaci Kiristoci da su yi amfani da wannan lokaci don addu’a domin zaman lafiya, tsaro da samun shugabanni masu adalci da tausayi.

Ta kuma bayyana cewa rashawa, son zuciya, rashin tausayi da almubazzaranci daga shugabanni na ƙara jefa ƙasar cikin mawuyacin hali.

Ta roƙi Allah ya ƙara ƙarfafawa dakarun tsaron ƙasar wajen yaƙar ‘yan ta’adda, tana mai fatan Nijeriya da Arewa za su ci gaba da zama masu ƙarfi da haɗin kai.

By ukarofi