Easter: Bishop Kukah ya yi kira ga Tinubu ya kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban malamin addinin Kiristanci daga jihar Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya yi kira ga shugaban ƙasa kan ya kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da dawo da tsaro a Nijeriya.

Kukah ya ya nuna damuwarsa ce cikin saƙonsa na ranar mai tsarki (Easter) ta mabiya addinin Kiristanci wanda a ciki ya yi wa shugaban ƙasa wannan roƙo.

A cikin saƙon nasa wanda ya aike wa da Manhaja, Kukah ya ce ana cigaba da kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

“Ina taya miliyoyin mutane ‘yan Nijeriya maza da mata,” ya faɗa. “Gare mu Kiristoci, wannan muhimmin abu ne ga addininmu. Wannan lokaci ne na murnar irin nasarar da Yesu ya yi galaba kan mutuwa.”

Kukah ya ce, “Wannan biki ya shafi fito da irin wahalhalun da mutane ke fama da ita a wannan ƙasa tamu na tsawon lokaci,” ya faɗa yana mai nuna damuwarsa game da yadda ake cigaba da kisan al’umma.

Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ƙungiyoyi ta’addanaci kama daga Boko Haram a yankin Arewa maso gabas wanda ya haifar da tashin hankali a jihohin Borno, Yobe da Adamawa wanda ya yaɗu zuwa Arewa ta tsakiya.

A kwanakin baya ne dai wasu masu ɗauke da makamai suka kai hari kan al’ummar jihar Fulato da Benuwai inda aka kashe mutane ɗaruruwa da lalata kadarori.

Wannan irin hare-hare dai kan zama wata barazana ga sha’anin samar da abinci wanda Kukah a saƙonsa na Easter ga shugaba Tinubu, ya ce, akwai buƙatar kare dukkan “haƙƙin bil’adama”. daga nan ne, ya buƙaci Tinubu da ya kawo wa ‘yan Nijeriya sauƙi daga irin halin yunwa da ake fama da ita.

Sannan Kukah ya koka game da ƙaruwar satar mutane a Nijeriya .

“A faɗin Nijeriya , a kullum, ana sace mutanen da ba su ji ba su gani ba da suke samun kansu cikin mawuyacin hali, domin ta ko’ina, daga Arewa zuwa Kudu, mutuwa ce ke yawo.”

Sai dai ya ce ba Tinubu ba ne ya haifar da matsalar tsaro, inda ya ce, akwai buƙatar ya sake dawawa da ‘yan Nijeriya fatan da suke da shi na samun zaman lafiya a ƙasar nan.

Daga ƙarshe ya ce, yana da tabbacin cewa da yawan ‘yan Nijeriya na son zaman lafiya da junansu. Sai dai ya ce cigaba da barin matsalar tsaro ta ta’azzara, zai kawo tarnaƙi ga burin kowacce gwamnati na kawo cigaba.

“A halin da ake ciki, al’umma na cikin damuwa a yayin da gwamnatin da jami’an tsaro ke zama kamar ‘yan kallo a yayin da mutuwa ke cigaba da yin barazana ga al’umma.”

“Muna cikin tsaka mai wuya, kuma babbar abin tambayar ita ce, shin cigaba da ta’azzara da tsaro ke yi a Nijeriya na nufin jami’an tsaronmu sun gaza kenan? Ko kuwa dai ana sadaukar da rayukan ‘yan Nijeriya ne ga wani abin bauta? Shugaban ƙasa, ya kamata ka ƙara miƙewa, a ƙarasa wannan aiki da kawo karshen wannan abin kunya da muke ciki,” ya bayyana.

Kukah ya ce, soke Yesu ya koyar da Kiristoci yadda za su fuskanci kowanne ƙalubale da ƙarfin guiwa.

By ukarofi