Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An buɗe babban masallacin Juma’a mai haɗe da cibiyar horar da limaman masallatan Juma’a wanda gidauniyar Sautus Sunnah ta gina a Katsina.
A jawabin sa shugaban gidauniyar kuma shugaban ƙungiyar Izala reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya ce wannan wuri an buɗe shi ne domin bada horo na musamman ga limamai da sauran malamai ta yadda za a riƙa yaɗa addinin Muslunci.
Ya ce wannan masallaci tare da cibiyar horar da limamai ba shine na farko ba, akwai irinsu da gidauniyar ta gina a faɗin jihar.
Da yake jawabi bayan da ya ƙaddamar da buɗe masallacin, gwamna Dikko Raɗɗa ya nanata ƙudirin gwamnatin sa na cigaba da ba addinin Muslunci gudummawa.
Ya bayyana cewa irin wannan gudummawa ne yasa gwamnatin jihar ta kafa hukumar Zakka da waqaf da kuma hukumar Hisbah a jihar.
Gwamnan sai ya roƙi malamai da su cigaba da saka Jihar Katsina addu’a, mu kuma a shirye muke mu karɓi kowane irin shawara da zai amfani al’ummar jihar.
Ya yabawa gidauniya kan ƙoƙarin da take na yaɗa addinin Muslunci a sassan jihar.
