NSCDC Gombe ta yi bankwana da kwamanda Gyama Gyawiya bayan ya yi ritaya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A wani biki na ban girma mai ƙayatarwa, hukumar NSCDC reshen Jihar Gombe, ta yi bankwana da Kwamandanta, Gyama Gyawiya, wanda ya yi ritaya bayan cika shekarun aiki da doka ta tanada.

Taron bankwana, wanda ya gudana a hedikwatar hukumar da ke Gombe, ya samu halartar ɗimbin manyan baƙi, ciki har da Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya samu wakilcin Laftanal Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya), kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na jihar.

Sanarwar da Kakakin hukumar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar ta bayyana cewa taron ya tara shugabannin hukumomin tsaro, manyan mutane, da jami’an NSCDC daga sassa daban-daban domin girmama Kwamanda Gyawiya, wanda ya kafa tarihin da ba za a manta da shi ba.

A jawabinsa na ban kwana, Gyawiya ya nuna godiya ga babban kwamandan NSCDC, Dokta Ahmed Abubakar Audi, bisa jagorancinsa da kuma damawa da shi wajen jagorantar hukumar a Gombe.

Har ila yau, ya godewa gwamnan Jihar Gombe da al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka ba shi tare da yabawa jajircewar jami’an hukumar wajen gudanar da ayyukansu.

Gyawiya ya yi kira ga jami’an NSCDC da su ci gaba da aiki da ƙwarewa da sadaukarwa don tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.

Bikin ya ƙunshi zaman ban girma inda aka yi ta yabon nasarorin da Gyawiya ya cimma, tare da gabatar da kyaututtuka daga masu riƙe da muƙamai daban-daban.

Hakimin Kamo na ƙaramar hukumar Kaltungo, tare da dattawan yankin, sun naɗa Gyawiya da lambar yabo ta “Hasken Kamo,” inda suka jinjina masa bisa gudunmawar da ya bayar wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban yankin.

Kwamishinan noma da kiwo na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle, ya yabawa Gyawiya bisa rawar da ya taka wajen warware rikicin manoma da makiyaya, yana mai cewa naɗin Hasken Kamo ya dace matuƙa da irin gudunmawar da ya bayar.

Mataimakin Kwamandan hukumar (DCC), Abubakar Muri, ya bayyana Gyawiya a matsayin shugaba mai kima, wanda taken sa na “Work na work” ya ƙarfafa ƙwazon jami’an hukumar.

A yayin da yake fara rayuwar ritaya, hukumar NSCDC ta Jihar Gombe ta yi masa fatan alheri, tana mai jaddada cewa tasirin jagorancinsa zai ci gaba da zama abin alfahari da darasi ga waɗanda ke tafe.

By ukarofi