Gwamnan Kano ya bankaɗo rarar miliyan N28 a albashin watan Maris

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinta na tsaftace harkokin biyan albashi ga ma’aikatan Jihar Kano, Gwmantin Abba Kabir Yusuf, ta yi nasarar bankaɗo kimanin Naira miliyan 27,824,395 na albashin watan Maris, 2025.

A ƙoƙarinsa na yin kwaskwarima ga tsarin biyan, Gwamna Abba ya kafa kwamitin sanya ido game da harkokin albashin ma’aikata a jihar.

Kwamitin zai yi aiki ne kafaɗa-da-kafaɗa da sauran masu-ruwa-da-tsaki da suka shafi ɓangaren don tabbatar da gaskiya da adalci.

Haka kuma zai sanya ido kan yadda ake biyan ma’aikata a ƙananan hukumomin jihar gami da daƙile ayyukan rashin gaskiya a yayin aiwatar da biyan albashi ga ma’aikata.

Bayan wani bincike ne aka gano kimanin ma’aikata 247 da kodai sun yi ritaya ko kuma sun rasu amma kuma sunayensu suna cikin waɗanda ke karɓar albashi.

Tuni aka gano maƙudan kuɗaɗen tare mayar da su asusun ƙananan hukumomin jihar, kamar yadda Sakataren yaɗa labaran Gwamnatin jihar, Musa Tanko Muhammad ya bayyana a wata takarda.

Ya kuma ce, hakan wata gagarumar nasara ce da gwamnatin ta samu duba da yadda ta ke ƙoƙarin tsare gaskiya da adalci ga ma’aikata da ma al’ummar jihar baki ɗaya.

By Babaji