Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Makarantar Babban Malami Madabo Islamiyya ta gudanar da taron yaye ɗalibai da suka yi saukar karatun Alƙur’ani a ranar Lahadi a ɗakin taro na gidan Mumbayya.
Shugaban makarantar kuma Darakta na makarantun Khulafa’urrashiduna dake jihar Kano guda 12, Malam Nassar Rilwan Ibrahim Babban Malami ya ce ɗalibai 173 ne maza da mata suka sauke Alƙur’ani da riwayar Hafsu da kuma guda 16 da suka yi riwayar warshu aka yaye.
Ya ce saukar karatu a makarantar wannan shi ne karo na 24 tun daga kafata, domin da an soma yinta da dare ne a 1960 a lokacin. Babban Malami na Madabo Malam Ibrahim daga baya kuma a 1983 Sheik Rilwan Ibrahim Babban Malami ya buɗe na karatun yamma kamar irin wannnan kenan ake tara samari maza da mata don koyar da su Alƙur’ani da sauran darussa na Islamiyya wanda yanzu suna da malamai guda 40.
Malam Nassar Rilwan Ibrahim ya ce yanzu haka makarantar tana da mazauni domin sun sami gudummawa daga Hajiya Mariya Sanusi ɗantata ta bada ginin makaranta mai ajujuwa takwas da makewayi guda huɗu da ofisoshi biyu.
Shi ma Bashir Mudi ya bada ginannen makaranta. Tsohon shugaban ƙaramar Hukumar Dala Marigayi Ali Yantandu shi ma ya sayawa makaranta wuri ya gina.
Ya ƙara da cewa daga waɗanda suka tallafawa makarantar akwai Samata Kabiru Gaya shi ma ya gina mata rukunin ajujuwa biyu.Tsohon Gwamnan Kano Ganduje shi ma ya bayar da tallafi na N10,000,000 an sai wurare na makarantar haka Alhaji Aminu Dantata shi ma ya bada N10,000,000 an fara gina wuraren da su, amma ba a kai ga kammalawa ba.
Ya ce yanzu matsalolin da suke fuskanta shine na ginin da suka fara ba a kammala ba suke so su ga an ƙarasa su da kuma gyara ginin da Kabiru Gaya da wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala suka yi musu don sun yi rauni suke son a yi musu kwaskwarima a inganta su.
Malam Nassar Rilwan Ibrahim ya ce sun kai takarda ta neman tallafin azo a ƙarasa musu wannan ginin makarantar ga zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano.Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin sa na wanda yake baiwa cigaban ilimi kulawa na musamman suna nan suna bibiya suna fatan Gwamna da Gwamnatinsa za su duba koke na wannan makaranta ta ga cewa ta share musu hawaye.
Ya ce tunda aka buɗe makarantar tasu a shekarar 1983 zuwa yanzu an sami nasarori har ana sauka ana yaye ɗalibai har karo 24 wanda a cikinsu akwai mahaddata akwai waɗanda sun zama Gwanayen ma na Alƙur’ani wannnan nasara ya samu ne bisa irin haɗin kai da iyayen yara ke bai wa makaranta suna godiya da irin haɗin kai da ake ba su.
Malam Nassar Rilwan Ibrahim Babban malami ya yi kira ga al’umma musamman wanda Allah ya horewa su riƙa taimakawa irin waɗannan makarantu na Islamiyya su ga cewar sun kawo gudummawa ta yadda karatun ‘ya’yansu da tarbiyyar su za ta gudana yadda ya kamata.
