Daga JOHN D. WADA a Lafiya
An shawarci mata su riƙa zuba jari a sana’oi da harkokin kasuwanci daban-daban don ba su damar dogara da kansu da kuma tallafawa iyalansu a koyaushe.
Babbar sakatariyar dindindin na ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da zuba jari na gwamnatin jihar Nasarawa, Hajiya Khadijat Nuhu Oshafu ce ta bada wannan shawara a lokacin da take tattaunawa da wakilinmu a ofishin ta dake ma’aikatar a Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Laraba na makon da ake ciki.
Ta ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la’kari da muhimmancin harkar zuba jarin a harkokin kasuwanci daban-daban a ƙasar nan musamman daga wajen mata don samun biyan buƙatu da kuma rufin asiri ta ribar da ake samu.
Babbar sakatariyar Hajiya Khadijat Nuhu Oshafu ta ƙara da cewa lokaci ya wuce da mace matan aure zanta riƙa dogara kacokan ga mijin ta inda ta ce akwai riba sosai da kuma samun rufin asiri a harkokin zuba jarin.
Ta kuma yi amfani da damar inda ta buƙaci waɗanda ke da niyyar zuba jari a harkokin kasuwancin su riƙa ziyaryar ma’aikatar don yin ragista don su samu cikakken izini da wasu damarmaki kafin su fara harkokin kasuwancin nasu don guje wa wasu matsaloli da ake fuskanta sakamakon ƙin yi ragista da hukumomi da suka dace a ma’aikatar.
Hajiya Khadijat Nuhu Oshafu ta kuma ba da mitsalin yadda saudayawa idan ire-ire mutanen dake kin yin ragistan dazarar suka samu matsala ne kadai zai su gudu su je ma’aikatar amma a lokacin bazasu iya samun biyan bukata ba don ma’aikatar ba ta san dasu ba.
Daga nan sai babbar sakatariyar na ma’aikatar kasuwanci masana’antu da zuba jari na jihar Hajiya Khadijat Nuhu Oshafu har ila yau ta yi amfani da damar inda ta yi kira ga na musamman ga gwamnatoci a duka matakai da sauran masu hannu da shuni cikin al’umma su rika tallafa wa waɗanda ke da sha’awar harkar zuba jarin musamman mata don acewarta dayawa cikin su suna so harkar wasu ma suna ciki dumudumu amma suna fuskantar karamci da rashin jarin fara harkar.
A ƙarshe zai ta yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da kokari da yake yi wajen kirkiro da shirye-shirye ingatattu ta hadin gwiwa da babban bankin Najeriya da na duniya da sauran hukumomi da suka dace don cigaba da tallafa wa dinbin mata da nakasassu da sauran su kana ta yi kira a yi koyi da gwamnatin na Injiniya Abdullahi Sule.
Binciken wakilinmu dai ya gano cewa tunda aka nata hajiya Khadijat Nuhu Oshafu mukamin babbar sakayariyar dindindin na ma’aikatar ne take ya gudanar da gangamin wayar da kawunan ‘yan uwanta mata musamman game da shiga duk wara harka da zasu taimaki kansu kuma a yanzu haka matan suna cigaba da yaba mata a kullun.
