Kotu ta tabbatar da hukunci kan farfesan da ya yi maguɗi a zaɓen Akpabio 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Kalaba, a ranar Laraba, ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Farfesa Peter Ogban, wanda aka ɗaure a shekarar 2021 saboda yin maguɗi a zaɓen Sanata domin amfanin Godswill Akpabio, Sanata daga Jihar Akwa Ibom.

Mista Akpabio, ɗan jam’iyyar mai mulki ta APC, shi ne Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya. Maguɗin ya faru ne a wani zaɓe da ya sha kaye kafin ya sake tsayawa takara a shekarar 2023, inda ya lashe zaɓen kuma aka zaɓe shi shugaban Majalisar Dattawa.

Mista Ogban, Farfesa a fannin kimiyyar ƙasa a Jami’ar Kalaba kuma jami’in sanar da sakamakon zaɓe a zaɓen 2019 a yankin Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, an ɗaure shi na tsawon shekaru uku a  babbar kotun jihar da ke Uyo saboda bayyana sakamakon zaɓe na bogi a ƙananan hukumomi biyu — Oruk Anam da Etim Ekpo — domin amfanin Mista Akpabio.

Wani lauya da ya halarci shari’ar a kotun ɗaukaka kara ya shaida wa Manhaja a yammacin Laraba cewa Kotun ɗaukaka ƙara ba wai kawai ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Ogban da ɗaurin shekaru uku ba, har ma ta soki rawar da ya taka a matsayin Farfesa wajen sauya sakamakon zaɓe cikin yaudara.

By ukarofi