Har yanzu ƴan gaban goshi suna fafutukar neman kai matatarmu ƙasa, inji Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban rukunin Kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce har yanzu matatarsu ta Dala biliyan 20 tana fuskantar ƙalubale a yayin da ta ke ƙoƙarin gudanar da harkokinta cikin salama.

Ya ce, a shirye ya ke wajen faɗa da duk wani yunƙuri na kai matatar ƙasa.

Shahararren Attajirin na Afrika ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da tawagar masu zuba jari a Legas, ƙarshen mako.

Ɗangote ya bayyana cewa, waɗanda suka samu kuɗi wajen shigo da mai Nijeriya a tsawon lokaci, sune waɗanda ke shirya wa matatar maƙarƙashiya.

Ya kuma ce, sune suka taimaka wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen cire tallafin man fetur, kuma daga bisa su ke ƙoƙarin murƙushe aikin matatar da ke ƙoƙarin sauƙaƙe wa al’umma a ƙasar.

Alhaji Aliko Ɗangote ya ci alwashin yaƙar manufofinsu na kai matatar ƙasa, ya na mai cewa zai yi hakan ne har sai ya yi galaba akansu.

A baya ne dai Ɗangote ya yi zargin cewa akwai wasu kamfanonin mai na ƙasa-da-ƙasa da ke ƙoƙarin daƙile tasirin sabuwar matatar, inda ake hana su wadataccen ɗanyen mai duk da cewa doka ta wajabta hakan.

By Babaji