Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da ƙudurori biyu daga cikin huɗu na dokar haraji da shugaban ƙasa Tinubu ya gabatar mata.
ƙudurorin sun haɗa da na dokar da ta shafi sauya tsarin hukumar tara haraji ta ƙasa da kuma samar da wata hukumar da za ta shafi tattara haraji na haɗin gwiwa tsakanin sassa daban-daban.
Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio, ya yi farin ciki da amincewa da ƙudurorin biyu, inda ya ce za su inganta harkar shugabanci da kuma zamanantar da yadda ake karɓar haraji da kuma raba shi a faɗin ƙasar.
“Waɗannan ƙudurori za su ƙara inganta harkar gudanar da gwamnati da kuma sauye-sauye kan yadda ake karɓar haraji,” inji shi.
Ya ƙara tabbatar da cewa za a kammala amincewa da sauran ƙudurorin biyu a gobe Alhamis.
Wannan doka ta haraji dai ta sha suka daga ’yan Nijeriya musamman ma shiyar arewacin ƙasar, inda ake kallon cewa tsarin tattara harajin zai mayar da yankin saniyar ware.
A watan Oktoban 2024 ne, shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar ƙudurorin dokar haraji huɗu domin yin zama da kuma amincewa da shi.
