FARFESA SHEHU ADO GARKI ƙwararre ne kan sarrafawa da samar da sababbin irin shuka a zamanance, wanda ya ke aiki a Cibiyar Binciken Noma da ke Samaru, wacce ta keƙarqashin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a Zariya.
A yayin ziyarar da jagororin cibiyar suka kai wa Hedikwatar Blueprint Newspapers Limited da ke Abuja, Editan Blueprint Manhaja, NASIR S. GWANGWAZO, ya samu zantawa da Farfesa Garki, wanda ya ware masa aya da tsakuwa kan matsayin da malaman Musulunci suka yi kan yi wa irin shuka barbara, don samar da sabon iri ko sauya masa fasali. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:
MANHAJA: Assalamu alaikum. Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka.
FARFESA SHEHU: Wa’alaika salam wa rahmatullah wa barakatuhu. Ni dai sunana Farfesa Shehu Garki Ado, kuma ni ma’aikaci ne a ma’aikatar binciken ayyukan gona, wadda take a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Wane kwamiti ne ka ke shugabanta?
To, ni yanzu haka Ina kula da kwamitin kariya daga haɗarin halittun da aka gyara ta hanyar ilimin kimiyya, wato ‘biosafety genetically modified organisms’. Kuma ni ne shugaba naƙwararrun da suka san hanyonin zaɓo sabbin iri na Nijeriya.
To, ga shi dai kun kawo ziyara a hedikwatar Blueprint a nan Abuja. Shin mene ne maqasudin wannan ziyarar?
Abinda ya ke tafeye da mu shine, mu sanar da jaridu game da ma’aikatar, su yayata ayyukan da wannan ma’aikar take yi, musamman ma sabbin hanyoyin bunqasa ayyukan gona da ake samarwa, kamar yadda muke fatan a ceƙasarmu tana wadata mutanen ta da abincin da za a ci, ba tare da an jeƙasashen waje an siyo ba.
A bayanin da ka yi a zaman da aka yi, mun ji ka yi bayani kan halacci ko haramci ta fuskar addini kan samarwa ko canza fasalin waɗannan irin shuka da a ke da su ta hanyar yi musu barbara ko fasahar zamani. Wane bayani za ka yi wa Blueprint Manhaja akan wannan?
Bayanin dai shi ne, Musulmi suna damuwa da abincin da ya kasance halal ne ko haram. Saboda haka akwaiƙungiyar Musulmai ta duniya da keƙasar Malesiya da suka gayyato manyan malamai na duniya da kuma manyan masana a ɓangaren ‘genetic modified organisms’, suka tattauna. Dagaƙarshe hukuncin da aka yi kan wannan shi ne, idan wannanƙwayar halittar da ake ɗauka, a canza wata da shi, idan ya kasance an ɗauko ne daga abinda yake na haram, aka sa a na halal, to wannan halal ɗin ya haramta. Misali, ba za a ɗaukoƙwayar halitta daga alade ba a saka a abincin da Musulmai za su ci a ce ya halal ta ba, wannan haramun ne. Amma idan daga abinda da ma halal ne Musulmai su ci aka ɗauko, aka gyara, aka inganta wani, to ya halalta.
To, ta yaya mutane Musulmai za su iya bambance ko gane wannan bayanin. Shin ku na haɗa wa da bayanin abinda aka haɗa irin da shi?
Kamata ya yi idan aka ce ga wannan iri ne, to mutum ya bincika ya gane da me aka haɗa shi, don ya tabbatar. Kuma shi da ma wannan iri ɗin tilas ne duk abinda za a yi da shi a gaya wa mutum don ya sani. Ya san wannan fa iri ne da aka haɗa. Haka dokarƙasa ta tanada. Idan aka kama mutum bai yi hakan ba, za a hukunta shi.
Mun gode.
Madallah, ni ma na gode.
