Masu garkuwa suka sare min hannu ba Musulmi ba, inji wanda abin ya shafa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani matashi mai matsakaicin shekaru da aka yanke wa hannu na hagu, a wani faifan bidiyo na baya-bayan nan ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa masu kishin Islama ne suka yanke hannunsa.

Wata majiyar tsaro ta ce, mutumin mai suna Lanlege Samuel Adewale, wanda ya zanta da jami’an tsaro bayan an kuɓutar da shi tare da ɗan uwansa, ya bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da shi tare da ɗan uwansa, a ranar Lahadin da ta gabata, a lokacin da suke kan babur zuwa Ogbe a ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi.

A cewar Adewale, a yayin da ya yi ƙoƙarin kaucewa sarar adda a wuyansa ne ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya yanke hannunsa na hagu.

Majiyar jami’an tsaron da ba ta so a bayyana sunanta ba, ta ce wanda aka yi garkuwa da shi ya ci gaba da cewa, a yunƙurin da ya yi na tserewa ne daga hannun masu garkuwa da mutane a dajin Babanla da ke aaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, cewa ɗaya daga cikin ‘yan ƙungiyar ya yanke hannunsa na hagu, har sai da tawagar jami’an tsaro ta haɗin gwiwa suka same shi suka kai shi asibiti.

Majiyar ta bayyana cewa, kafin fafatawar da suka yi ta kuɓuta, masu garkuwa da mutanen sun tilastawa Langele da ɗan uwansa zuwa maɓoyarsu a dajin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, ta dajin Oke-Ere/Okoloke da ke Yagba yammacin jihar Kogi, inda suka kwashe kwanaki biyu.

“Masu garkuwa da mutanen sun kasance masu tsaurin ra’ayi kuma suka ƙi amincewa da ‘yan uwanmu, shi ya sa muka yi yunƙurin tserewa, kuma na yi ta fusata su har suka yi min rauni a ƙafa na da hannu sannan suka yi watsi da ni, ina godiya ga tawagar jami’an tsaro da suka kai ni asibiti.

“Hatsarin da ya afku a hannuna ba shi da alaƙa da jita-jitar da ake yaɗawa cewa nasu ikirarin jihadi ne na ƙasar Yarbawa, tun daga wasu jihohi,” inji shi.

By ukarofi