Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Asusun Kula da ƙananan Yara na Majalisar ɗunkin Duniya ya ce, Nijeriya a yanzu ta zama ƙasar da ke da nauyin yara masu fama da tamowa a Afirka.
Hukumar ta ƙasa da ƙasa ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo ranar Talata, inda ta ƙara da cewa a halin yanzu biyu ne daga cikin yara 10 da abin ya shafa ke samun magani.
Ya ce, tare da kimanin yara miliyan biyu a Nijeriya da ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, ƙasa mafi yawan baƙar fata a duniya ita ce ta biyu a yawan yara ƙanana a duniya.
“Nijeriya ce ƙasa ta biyu mafi girma na nauyin yara ƙanana a duniya, inda ake da kashi 32 cikin ɗari na yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.
“Kimanin yara miliyan biyu a Nijeriya na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki (SAM), amma a halin yanzu biyu daga cikin yara 10 da abin ya shafa ana kai musu magani.
“Kashi bakwai na matan da suka kai shekarun haihuwa suma suna fama da rashin abinci mai gina jiki,” inji ta.
UNICEF ta bayyana rashin abinci mai gina jiki a matsayin kai tsaye ko kuma sanadin kashi 45 cikin 100 na mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.
Ya yi bayanin cewa adadin shayar da jarirai nonon uwa zalla bai samu kyautatuwa ba cikin shekaru goma da suka gabata, inda kashi 17 cikin 100 na jarirai ne kawai ake shayar da su nono a cikin watanni shida na farkon rayuwarsu.
“Kashi 18 bisa ɗari na yara masu shekaru shida zuwa watanni 23 ba su samun isasshen abinci,” inji ta.
