Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo; tsohon shugaban ƙasa, Abdulsalami Abubakar; gwamnoni na cikin waɗanda ake sa ran za su halarci bikin ƙaddamar da littafin tarihin siyasar tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.
Littafin mai suna “Being True to Myself”, wani tarihin siyasa ne na Lamido, jigo a jam’iyyar PDP, kuma za a gabatar da shi ga jama’a a Abuja cikin mako mai zuwa.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja ranar Talata, Shugaban kwamitin shirya taron, Sanata Mustapha Khabeeb, ya bayyana taron a matsayin wanda zai “fitar da haƙiƙanin labarin siyasar Nijeriya” tun daga ƙarshen jamhuriya ta biyu, ta zamanin mulkin soja, zuwa haihuwa da kuma jamhuriya ta huɗu.
Ya ce, tsohon Janar Abdulsalami ne zai jagoranci taron, inda Obasanjo zai kasance babban baƙo na musamman.
Sanata Khabeeb ya kuma ce tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Dr. Iyorchia Ayu ne zai duba littafin.
Da yake bayyana abin da masu karatu za su yi tsammani, shugaban ya ce littafin tarihin rayuwar ya ba da labari mai ban mamaki game da yadda ake tafka maguɗi, cin amana, da gwagwarmayar mulki da suka haifar da tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, ya ƙara da cewa “wani tsarin siyasa ne da ke ɗaukar ruhin mulkin Nijeriya da tarihin dimokuraɗjyya.”
Ya ci gaba da bayyana cewa littafin ya zurfafa a cikin rayuwar Lamido a matsayin ɗan siyasa, ma’aikacin gwamnati, kuma dattijo.
