Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Manajan ciniki na kamfanin FMN Flour Mills North, Samuel Smart ya bayyana cewa ƙarƙashin tsarin Cooperate Social Responsibility CSR na taimakawa al’umma da wannan kamfani ke aiwatarwa a kodayaushe dubban mutane ne suka samu tallafin abinci musamman a watan azumin Ramadan da ya gabata da sauran lokuta na yin abubuwa na taimakon ilimi da kayan buƙatu na rayuwa a ƙoƙarin kamfanin na kyautatawa al’umma da kuma masu hulɗa da shi a ko da yaushe.
Manajan sayar da kayayyaki na FMN, Samuel Smart ya bayyana haka ne a lokacin taron da kamfanin ya shirya a ranar Talata domin kyautatawa manyan dilallan kamfanin da kuma gabatar da sabbin irin kayayyakin da kamfanin ya inganta shi cikin irin kayayyakin abinci da yake sarrafawa don masu hulɗa da kamfanin a birnin Kano a makon da ya gabata.
Haka kuma ya ce FMN zai cigaba da karɓar shawarwarin abokan hulɗarsa a ko da yaushe domin dai kyakkyawar mu’alama domin inganta kayyayaki.
Ya kuma yaba wa dilolin kamfanin da masu sarin kayan da masu zubawa a shago har ma da masu sayen kayan kamfanin domin amfanin yau da kullum a gidajen su ko ma’aikatunsu, wanda kuma hakan ne ya sa wannan kamfani ke cigaba da wanzuwa da kuma ɗaukar matasa aikin yi a Kano da ma Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
Taron dai ya samu halartar manyan shugabannin da ɗimbin ma’aikatan FMN sai kuma manyan dillalan kamfanin daga sassa daban-daban na jihar Kano da maƙwaftansu a wannan taro da Samuel Smart ya sha alwashin shirya taruruka domin samun kyakyawar dangantaka da abokan kasuwanci shi da ma sauran al’ummar Nijeriya.
