Daga HARUNA AKARAɗA a Kano
Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar kare rajin Hausawa a Nijeriya ya yi bayani kan matsayarsu bisa wasu matsaloli da suke damun Hausawa a ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar Abdullahi Abdullahi ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Litinin.
Taron wanda aka gabatar da shi a gaban wasu manyan ƙusoshi na ƙungiyar inda ya bayyana matsalolin da cewa wani abu ne da ya daɗe yana ci musu tuwo a ƙwarya, inda ya bayyana matsalolin kamar haka:
Ana yunƙurin kore samuwar Bahaushe amma ana ƙoƙarin tabbatar da samuwar ƙabilar Inyamuri, Bayarabe da Bafulatani.
Haka nan ga irin ta’addancin da ake yi wa Bahaushe a ƙasarsa ta gado, inda ya kawo misalai da kashe Sarkin Gobir da ƙona Hausawa da ransu cikin mota da Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda suka yi a ranar da Buhari ya je Legas ƙaddamar da littafi, yanzu ina labarin ya kwana, kuma shin an kama masu hannu cikin wannan ta’addancin?, sannan ya batun labarin da Yan ta’adda suka baiwa karnukansu jarirai suka cinye, da matan da suka yi wa fyaɗe a masallaci? da kuma Hausawan da aka ƙone su da ransu a jihar Edo ta kudancin ƙasar nan, wake magana ko da ƙungiya ce a kansu?.
Shugaban Hausawan ya ƙara da cewa “wannan ne dalilin da ya sa dole ne mu Hausawa mu haɗa kai don mu ƙalubalanci masu aikata hakan da masu ɗaure musu gindi cikin malamai, ‘yan siyasa da sarakunan ƙasar Hausa dama ta su ƙungiyar dake basu kariya,’ ya ƙara da cewa.
“Akwai wani taron sulhu da wasu daga cikin shugabannin Fulani da malamai suka yi na neman sulhu sannan a ba su muƙamai a gwamnati, to wannan shine babban kuskure da gwamnati da ƙungiyar za ta yi, domin daga ranar da ta bai wa ‘yan ta’adda to muma daga ranar za mu biyo musu ta wata hanyar. A garin nan muka ga wani malamin addini yana cewa “su Turji mayakansu ne na daji, su kuma na birni ke nan.”
Shugaban ya ƙarƙare da cewa “akwai masu cewa kwangilar ce aka baiwa masu gwagwarmayar Hausawa, inda ya bayyana maganar a matsayin rainin hankali tun da suna ganin cewa Bahaushe ba shi da tunanin ya nemawa kansa mafita.
