Ɗaukar malamai 1000 aiki: Gwale ce kan gaba a bunƙasa harkar ilimi a Kano – ES Mukhtar

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA A KANO

An bayyana cewa ɗaukar malaman makaranta sama da 1,000 da Shugaban ƙaramar Hukumar Gwale Hon. Abubakar Mu’azu Moju ya yi daga hawansa zuwa yau, ya nuna cewa ƙaramar Hukumar Gwale ita ce kan gaba wajen bunƙasa ilimi a ƙananan hukumomi 44 da ake da su a jihar Kano, wannan kuma na da alaƙa ne da yadda gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka ba ilimi muhimmanci a lokacin mulkin su na jihar Kano kamar dai yadda Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Gwale Hon. ES Mukhtar Inuwa ya tabbatar da wannan a lokacin zantawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke cikin birnin Kano.

ES Mukhtar Inuwa ya bayyana cewa ƙaramar hukumar Gwale ita ce ƙaramar hukumar da babu irin ta ta fuskar tasirin ilimi idan aka yi la’aƙari da malamai da masana su ke a ƙaramar hukumar ga kuma makarantu tun daga makarantar rainon yara har zuwa manyan jami’o’i na cikin ƙaramar hukumar Gwale kuma gwale ce ƙaramar hukuma da za a haife ka kasamu damar yin karatu har kazama Farfesa baka fita wata ƙaramar hukumar ba in ma da wata ƙaramar hukumar mai irin wannan baiwar to Gwale ce kan gaba.

Kuma hakance ta sa shugaban ƙaramar hukumar Gwale ƙaramar Hukumar gwamna Abba Kabir Yusuf ta sa shugaban ƙaramar hukumar ya jajirce wajen bunƙasa ilimi da ayyukan cigaba ta kowane fanni wanda shi ne ya bada dama na ɗaukar malaman kashi-kashi da kwamiti da kuma dama da aka bai wa masu ruwa da tsaki na kawo sunayen matasa da takardun na karatu domin ɗaukar su aiki da shugaban ƙaramar hukumar Hon Muazu Moju ke yi ko da yaushe. Inda kuma ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar kan goyon bayan da hukumar ilimi LEA Gwale ke samu ta hanyar gyaran makarantu da kayan aiki da kuma inganta rayuwar malamai da ma’aikata daidai da manufar gwamnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf.

By ukarofi