Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Hon. Sunusi Kata Madobi, jagoran gwagwarmayar neman a biya tsofaffin kansiloli haƙƙinsu kuma tsohon kansila a ƙaramar Hukumar Madobi, da gwamnatin baya ta ƙi biyansu a zamanin gwamnatin da ta gabata 2015 zuwa 2023 wanda kuma yanzu wannan gwamnati ta Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince za ta biyasu maƙudan kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira biliyan 13 wannan abin a yaba ne kamar yadda babban baƙo mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo kuma wanda ya wakilci gwamnan Kano a taron ya bayyana haka, Hon Kata Madobi tsohon kansila a ƙaramar hukumar Madobi ya ce wannan abin a yabawa gwamnatin Kano ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamarade Abdulsalam Gwarzo kamar yadda ya bayyana a ranar Talatar nan da ta gabata a babban ɗakin taron na gidan gwamnatin Kano.
Shi ma a jawabinsa gwamnan Kano da mataimakinsa ya wakilta ya ce wannan biya an kasa shi kashi-kashi ne wanda za a fara biyan tsofaffin kansilolin a wannan wata na Mayu inda za a yi wata uku ana biyan ƙasan farko sai kuma na biyu haka za a yi tayi har a biyasu gabaɗaya.
Sai dai kuma mataimakin gwamnan Kano ya bayyana takaicinsa akan yadda gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ƙi biyan kansiloli haƙƙinsu harda kansilolin su na Gandujiya su ma ba su samu haƙƙinsu ba ga kuma irin yadda ‘yan fansho suka yabawa aya zaƙi a zamanin gwamnatin da ta gabata da dai sauran matsaloli da al’ummar Kano su ka fuskanta a gwamnatin baya.
A ƙarshen taron ya samu halartar tsofaffin kansiloli na ƙungiyar su a matakin ƙasa da na jiha inda kuma aka karrama wasu fitattun shugabani a kan ƙoƙarin da suka yi a ciyar da al’ummar su gaba kaɗan daga ciki akwai shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar Kano kuma shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada Hon Saadatu Salisu Yushau sai kuma Hon Anas Muhktar Bello ɗanmaliki shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa da ke arewacin jihar Kano da sauransu.
