Bincike: Shin Turaren wuta na da haɗari ga lafiyar mutum?

Spread the love

Tare da MARYAM BATOOL

Iƙirari: Wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin Instagram ya yi iƙirarin cewa Turaren Wuta na da matukar hadari ga rayuwar ɗan Adam.

Wannan iƙirari ya jawo martani da dama inda aka samu sharhi dari biyar da biyu, Wanda suka nuna masa alamar so dubu sha daya da dari uku, masu kallo dubu dari huɗu da talatin da biyu, sannan mutane dubu sha tara da dari takwas suka yada bidiyon. Mutane da dama sun yarda da iƙirarin, Inda suka ce gaskiya ne kuma turaren wuta ba shi da kyau ga lafiya.

Ko da yake kunna turaren wuta al’ada ce da ake yi a Najeriya da wasu kasashe domin ibada ko nishadantarwa, binciken kimiyya ya nuna cewa yana iya jawo matsaloli ga lafiya, musamman idan ana yawan shakar sa ko amfani da shi a kai a kai.

An shafe ƙarni da dama ana amfani da turare a sassa daban-daban na duniya don al’adun addini, tunani mai nutsar da hankali, ko don jin dadin kamshi. Duk da cewa turaren na iya haifar da nutsuwa da jin daɗi, wasu bincike na kimiyya sun bayyana hatsarurruka da ke tattare da shakar hayakin sa, musamman ga mata da ke amfani da kamshi a kullum.

Turaren wuta na zuwa a siffofi iri-iri kamar sandal, joss stick, kwallo, zobe, gari, igiya, dutse ko kwal.

Tabbatarwa: Binciken PRNigeria Fact Check ya nuna cewa turaren wuta na fitar da sinadarai masu guba da hadari ga lafiya, irin su:

-Particulate Matter (PM): Turaren wuta na fitar da tarkace a cikin iska fiye da sigari—kimanin 45 mg/g idan aka kwatanta da 10 mg/g na sigari.

-Volatile Organic Compounds (VOCs): Sinadarai irin su benzene, toluene, da formaldehyde suna cikin hayakin turaren wuta.

Sakamakon cigaban bincike na PRNigeria ya nuna cewa shakar wadannan sinadarai na iya haddasa:

-Matsalolin Numfashi: Kara hadarin kamuwa da asma, COPD (cutar gajeren numfashi), da sauran cututtukan numfashi.

-Ciwoka Masu Shafar Zuciya: Amfani da turaren wuta na dogon lokaci yana da nasaba da kara hadarin kamuwa da cututtukan zuciya.

-Ciwon Daji(Cancer): Ana danganta amfani da turaren wuta da yawan kamuwa da cutar daji (cancer) a hancin sama, baki, makogwaro da huhu.

Shawarwarin Amfani Da Shi:

-A Samu Iska Mai Yawa: A kunna turare a waje ko a daki mai iska domin rage hayaki.

-A Rage Yawaita Amfani Da Shi: Kada a yi amfani da shi akai-akai ko na dogon lokaci.

-A Yi Amfani da Madadin Shi: Irin su na’urar turare ko turaren daki na ruwa.

– A Kula da Masu Rauni: Kada a kunna turare a kusa da yara, tsofaffi, ko masu fama da cututtuka na zuciya da numfashi.

Kammalawa: Binciken PRNigeria ya tabbatar da cewa, ko da yake turaren wuta ba a bayyana shi a matsayin barazana mai girma kamar sigari ba, yana da matukar muhimmanci a fahimci hatsarurrukan da ke tattare da hayakinsa kamar yadda binciken kimiyya da dama suka nuna.

Hukunci: PRNigeria ta tabbatar da cewa iƙirarin cewa turaren wuta na da hadari ga lafiya gaskiya ne.

By ukarofi