
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon ďan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya haďu da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i a Amurka ta yayin taron ‘Cambridge Africa Together’ karo na 11, wanda aka gudanar a Jami’ar Cambridge.
An sanya El-Rufa’i a matsayin ďaya daga cikin masu gabatar da jawabi a taron, wanda ya hada manyan jagorori a Afirka, manyan malamai da masu kokarin kawo sauyi.
An hango ƴan siyasa biyun suna tattaunawa a tsakanin su duk da cewa ba a san hakikanin abinda suka tattauna ba.
Saidai hotunan wajen taron sun haifar da cece-kuce ganin cewa Obi da El-Rufa’i suna daga cikin wadanda ke da tasiri ga siyasar Nijeriya musamman na nan gaba.
A kwanan ne El-Rufa’i ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulki, APC zuwa SDP, lamarin da ya sa ake ganin ya ķulla alaķar siyasa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Hadakar ƴan siyasar waje guda na nufin yunķuri na karbe mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.
