
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamitin kula da ciyarwa na Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya, NAHCON karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Kabir, ya gudanar da aikin duba rumbun abincin maniyyata a Madina.
Jami’ar yada labaranta, Suwaiba Ahmed ta fadi hakan a wata takarda, ranar Juma’a
Ta ce, kwamitin ya yi hakan ne da nufin tabbatar da shirin ciyarwa ya kammala domin amsa bukatun abinci na maniyyatan Nijeriya, wanda ya mayar da hankali wajen tsafta da inganci abincin gami da wajen da aka ajiye shi.
Wuraren dafa abinci guda bakwai ne aka ware wa maniyyatan, inda aka tabbatar da tsaftarsu da kayayyaki da aka saka acikinsu.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitin sun gana da ƴan kwangilar da aka bai wa aikin abincin inda suka yi masu korafi game da tsarin shirya abincin, lamarin da suka bukaci a ingata saboda rashin gamsuwa da nagartarsa.
