
Daga BELLO A. BABAJI
Taron bikin karrama jaruman fina-finai na tashar Africa Majic karo na 11 ya karrama tsofaffin jaruman fina-finai Nijeriya, wato Malam Sani Mu’azu da Nkem Owoh na Nollywood, ranar Asabar.
Sani Mu’azu wanda tauraro ne kuma mai bada umarni, ya taba zama Shugaban kungiyar ƴan fim ta ƙasa, wato MOPPAN.
Ya kuma samu kyautar ne a sakamakon dadewarsa ya na bada gudumawa ga harkar fim wanda ya shafe sama da shekaru 30 ya na yi musammana Kannywood.
Malam Sani ya mika godiyarsa ga waɗanda suka shirya taron na AMVCA na 11 da goyon bayansu ga ciyar da Kannywood gaba.
