Gwamnatin Katsina za ta sa ƙafar wando ɗaya da masu cin zarafin ‘ya’ya mata da ƙananan yara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan Shari’a,Barista Fadila Muhammad Dikko ta yi wannan gargaɗi ne a jawabin ta wajen taron karawa juna sani a kan cin zarafin bil’adama.

“Ba zamu lamunci cin zarafin al’umma ba musanman ya’ya mata da ƙananan yara a jihar” ba inji Fadila.

Ta bayyana cewa sun shirya taron ne domin tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi cin zarafin ‘yan Adam tare da wayar da kan jama’a yadda zasu kai koken su ga hukumomi domin bi masu haƙin su,amma su tabbatar suna da cikakken shaida tare da hujjoji.

Kwamishinan tace tuni gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya ma dokar kare haƙin bil’adama hannu domin hukunta duk wanda aka aikata wannan laifi.

Fadila ta kuma sanar da cewa taron da suka haɗa da lauyoyi, alƙalai, jami’an tsaro,da sauran ma’aikatu za su tattauna a kan gano matsalolin da ake fuskanta gurfanar da masu laifi a gaban kotu .

“Haka kuma taron zai tattauna kan musabbabin abin da ke kawo tsaiko wajen gudanar da shari’ar”inji kwamishinan.

By ukarofi