Duk ɗan Arewa na da hannu a gyaran Arewa – Ahmad Mu’azu

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI Jos

An bayyana muhimmancin haɗin kan al’ummar Arewa, ba tare da nuna bambancin addini ko siyasa ba, shi ne abin da zai kawo maganin matsalolin da ke addabar wannan yanki na ƙasar nan. Don haka lallai masu faɗa a ji da shugabannin yankin Arewa su haɗa kansu, su daina raba kan al’umma, saboda wasu dalilai na son zuciya.

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, wanda ya taɓa riƙe shugabancin Jam’iyyar PDP na ƙasa, Ahmad Adamu Mu’azu, shi ne ya yi wannan kiran a yayin wani babban taron ƙungiyar raya al’ummar Jasawa ta JCDA, da aka gudanar a Jos, wanda aka shirya domin karrama wasu fitattun mutane da suka taimakawa cigaban garin Jos.

Ahmad Mu’azu ya bayyana cewa, idan ýan Arewa za su kawar da bambance-bambancen da ke tsakanin su, su zauna su dubi matsalolin da ke damunsu, babu shakka za su gano bakin zaren yadda za a warware su.

Ya ce, “Gyaran Arewa ba aikin gwamnoni ba ne kawai, haƙƙin dukkan mu ne, ýan siyasa, masu muƙamai, masu arziƙi, ma’aikata, talakawa, da mata da matasa. Duk wani ɗan Arewa, na da hannu wajen gyaran Arewa, da samar da cigaba, a duk wani matsayi da yake.”

Sauran manyan baƙi a taron da suka haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Filato, kuma Sanata mai wakiltar Shiyyar Filato ta Kudu, a Majalisar Ƙasa, Simon Lalong, da babban sakataren Jama’atu Nasril Islam, Farfesa Khalid Aliyu Abubakar sun ƙarfafa muhimmancin zaman lafiya da girmama juna a tsakanin ýan Arewa.

Ƙungiyar Raya Al’ummar Jasawa ta JCDA, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Isyaku Inuwa Ɗan Anacha ta karrama wasu fitattun mutane da suka daɗe suna ba da gudunmawa ga al’ummar garin Jos da Jihar Filato baki ɗaya. Waɗanda suka haɗa da tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai Ahmad Idris Wase, da babban sakataren Jama’atu Nasril Islam, Farfesa Khalid Aliyu Abubakar, babban ɗan kasuwa Alhaji Murtala Laushi, da Alhaji Salisu Umar Ɗanzaki, tsohon ma’aikacin harkokin ƙasashen waje, da kuma Alhaji Hassan Sallau (Teacher), tsohon ma’aikacin gwamnati.

Taron ya kasance wani dandali na haɗin kan Jasawa da duk wani mai faɗa a ji da yake tutiya da garin a matsayin tushen sa, musamman daga ɓangaren Hausawa musulmi.

By ukarofi