Sojoji sun kama sanannen ďan ta’adda da ķwato makamai a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Shiyya ta 3 na Rundunar Atisayen SAFE HEAVEN da haďin-gwiwar Hukumar Leķen asiri, sun kama shahararrun ƴan bindiga biyu da masu garkuwa da mutane a yankin Karamar Hukumar Barikin Ladi dake Jihar Filato.

Jami’in Hulďa da Jama’a na dakarun, Manjo Samson Nantip Zhakom a wata takarda, ya ce an gudanar da atisayen sirri ne a safiyar ranar Lahadi a yankin Marit Mazat, inda aka yi nasarar kama ďan bindigar kuma mai garkuwa da mutane, wato Yahaya Adamu.

Ya ce, a samamen da jami’an suka kai, sun kuma cafke wani babban ďan bindiga da ake nema ruwa-a-jallo mai suna Sa’eedu Haruna, inda suka ķwato bindigar Ak47 da mazubin alburusai gami da wata wayar hannu kirar ITEL.

Binciken da aka gudanar gabannin kamen ya nuna cewa, waɗanda aka kama da masu taimaka musu suna da hannu a aikata manyan laifuka a yankunan Gashish da Kurra Falls dake jihar da kuma Gwantu da Fadan Karshi a Karamar Hukumar Sanga na Jihar Kaduna.

Hukumomi sun tabbatar da cewa masu laifin suna hannu kuma sun fara amsa wasu daga cikin laifukan da ake tuhumar su da aikatawa, yayin da kuma ake kokarin kamo sauran ƴan bindigar da ķarin wasu makamai.

Dakarun na SAFE HEAVEN sun yaba wa mazauna yankunan bisa hadin-kai da suke ba su tare da nuna muhimmancin hakan wajen dakile ayyukan ta’addanci da ke bazarana ga zaman lafiyar al’umma.

Haka kuma sun yi kira ga jama’a da su rika ruwaito musu dukkan wani abin zargi da suka gani, wanda hakan zai taimaka musu wajen tattara bayanai akan ayyukan ta’addancin yankunan.

By Babaji