Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗanja Hon shamsuddeen Abubakar Dabai ya gabatar da ƙudirin,a zaman Majalisar, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar RT Hon Nasiru Yahaya Daura.
Buƙatar ɗaga darajar asibitin ya biyo bayan cunkoso na yawan jama’a marasa lafiya da ake samu a asibitin,kuma duk wata babban allura ba za a iya duba su ba sai dai a je Funtua ko Zaria.
Saboda haka ɗan majalisar ya buƙaci a samar da babban asibiti a garin Ɗanja, hakan a cewar sa zai taimaka ma harkokin kiwon lafiya a ƙaramar hukumar tare da bunƙasa su .
Shima ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɓatagarawa Hon Tukur Iliyasu Shaguna ya gabatar da ƙudirin tunatar wa,na buƙatar ci gaba da aikin sanya wutan lantarki masu amfani da hasken rana a garin Tsuntsuwa cikin mazaɓar Ɗanɗagoro.
Harwala yau a zaman Majalisar,ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar ingawa Hon, Abubakar Suleiman Tunas ya gabatar da ƙudirin samar da kayan aiki a babban asibitin garin ingawa.
Bayan doguwar muhawara kan ƙudurorin a zauren Majalisar, majalisar ta amince dasu,sai kakakin majalisar ya umarci akawun majalisar da ya tura ma ɓangaren zartarwa domin ɗaukan mataki akai.
