
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta aika da sakon gayyata ga tsohon shugaban mayakan yankin Neja-Delta, Chief Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, bisa zargin sa da wulakanta naira da rashin mutunta lamuran da suka shafi kuďi.
Sahara Repoters ta ruwaito cewa, a farkon makon nan ne aka tabbatar da takardar sakon ta isa gare shi, inda kawo yanzu ake jiran amsarsa game da lamarin.
Wata majiya ta ce, gayyatar ba ta nufin samun damar kama shi, saidai ďaya ce daga cikin hanyoyin da doka ta shar’anta na yin bincike a kai.
Hakan ya biyo bayan bayyana wani faifan bidiyo da aka ga Tompolo ya na bikin cikar sa shekaru 54 a watan Afrilu, inda aka ga ya na rawa yayin da wani mutum ya ke masa likin takardun nairori ƴan dubu-dubu, wanda yin hakan saba wa doka ne sashe na 21 na Babban Bankin Nijeriya, CBN.
Dokar ta bada damar kama wanda aka samu da saba mata ko kai mutum gidan yari ko duka biyun.
A sanarwar da ta fitar ranar Litinin, EFCC ta ce za a gudanar da bincike ne akansa duba da cewa babu wanda ya fi karfin doka.
