Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wasu matasa a garin Yanmaulu da ke ƙaramar hukumar Ɓaure a jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga kan suna buƙatar ganin an yiwa Zulaihatu Sidi adalci.
Muhammad Abdullahi wanda ya jagoranci zanga-zangar ya faɗawa manema labarai a garin Yanmaulu cewa yau kusan shekara ɗaya kenan da yan ta’adda suka yi garkuwa da Zulaihatu da yaron ta.
Garin Yanmaulu na cikin yankin masarautar Daura ne a jihar Katsina.
Mako guda da garkuwa da su Zulaihatu aka sako su bayan an biya Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa duk da haka sai da suka yi mata fyade kamar yadda jagoran zanga-zangar ya faɗa.
Muhammad ya ƙara da cewa mutane 8 aka Kama da ke da hannu akan garkuwa da wannan mata ƙarƙashin jagorancin ɗaukacin ƙauyen Mantau kuma wakilan Hakimin Yanmaulu mai suna Iliya Mantau da ake zargi da jagorancin ta’addan cin.
To sai dai mai magana da yawun masu zanga-zangar ya yi zargin cewa yayin da aka gurfanar da masu laifin gaban kotu, masarautar Daura na nan na ƙoƙarin ganin an saki dagacin ƙauyen.
“Kan haka ne muka fito mu nuna damuwar mu da wannan yunƙuri da masarautar ke ƙoƙarin yi”inji Muhammad.
Sai sukai kira ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya shiga cikin lamarin domin ganin anyi ma wannan mata da yaron ta adalci.
Da yake lamarin ya shafi masarautar Daura, manema labarai sun tuntuɓi Sarkin labarai game da zargin da a kayi wa masarautar amma yayi gum da bakin sa.
