Wararrun ‘yan majalisar dokokin Zamfara sun zargi Gwamna Dauda da almundahana

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wararrun ‘yan majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Hon. Bashir Aliyu Gummi sun zargi gwamna Dauda Lawal da kakakin majalisar, Bilyaminu Ismail Moriki da karkatar da kuɗaɗe kimanin miliyan 800 duk wata da sunan aiki na musamman.

Majalisar ƙarƙashin kakakin majalisar Hon. Bashir Aliyu Gummi a zamansu na ranar Talata sun bayyana matakin a matsayin cin hanci da rashawa.

Sun bayyana hakan ne a zaman nasu wanda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Aliyu Ango Kagara mai wakiltar Mafara ta kudu yayi wannan zargin.

Kagara ya buƙaci majalisar ta binciki mutanen biyu, kakakin majalisar Moriki da gwamna Dauda Lawal kan lamarin.

Hakazalika Hon. Faruk Musa Dosara mai wakiltar Maradun da Hon. Amiru Ahmed Keta mamba mai wakiltar Tsafe ta yamma da Hon. Barr. Bashir Abubakar Masama mai wakiltar yankin Bukkuyum ta Arewa a lokacin da suke bayar da gudunmuwar su kan lamarin sunce Naira miliyan 800 da ake cirowa a duk wata a cikin asusun ajiya na tsawon watanni 23, idan aka yi amfani da su ta hanyar da ta dace, za a ceto babban birnin jihar Gusau daga matsalar ƙarancin ruwan sha da ake fama da ita a halin yanzu wanda ya tilasta wa mazauna garin sayen jarka lita 25 a tsakanin N300 zuwa N500.

Sun bayyana cewa wani ɓangare na kuɗaɗen kuma da sun yi wasu abubuwa da dama da za su ciyar da jihar gaba.

Daga nan sai shugaban majalisar, Bashir Aliyu Gummi, ya miƙa batun ga kwamitin Adhoc na majalisar domin gudanar da bincike tare da miƙa rahoton ga EFCC da ICPC domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.

Hon. Gummi da ya jagoranci majalisar yayi Allah wadai da irin halin da gwamnatin gwamna Dauda Lawal ta yi na watsi da ɗaliban Zamfara a ƙasar Cyprus da ke tilasta musu shiga cikin mawuyacin ayyukan ƙwadago tare da fuskantar barazanar korarsu duk kuwa da roƙon da iyayensu suka yi ga gwamnati kan ta daidaita da mahukuntan Makarantar don biya musu kuɗaɗen makaranta.

Sun koka da yadda ɗalibai mata suke fuskantar irin wannan wahala a Ƙasar ta Cyprus.

“Maimakon haka gwamnan ya yi amfani da kuɗin gwamnatin jihar ne wajen halartar bikin yaye ɗansa a ƙasar Ingila tare da ‘yan uwansa da abokansa”.

Majalisar ta yi kira ga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da sauran ƙungiyoyin fararen hula da gwamnatin tarayya da su shiga tsakani domin ceto ɗaliban da suka koma tamkar marayu a Ƙasar ta Cyprus.

By ukarofi