APC ta dakatar da ɗan majalisa da wasu mutane tara a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL A GULMA a Kebbi

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta dakatar da tsohon ɗan majalisar wakilai Muhammad Shehu Koko wanda ya wakilci ƙananan hukumomin Maiyama da Koko a zauren majalisar a baya tare da waɗansu shugabnnin jam’iyyar a ƙaramar hukumar Koko.
Bayanin dakatarwar yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar ta Koko Muhammad Maibarga da shugaban ƙaramar hukumar ta Koko Honarabul Sirajo Usman Koko da waɗansu shugabnnin da ke da ruwa da tsaki a jam’iyyar na ƙaramar hukumar Koko.
Takardar ta bayyana cewa an dakatar da waɗannan mutanen ne bisa ga zargin su da ake yi na aikata waɗansu abubuwan da jam’iyyar APC ba ta yarda da su ba da suka haɗa da yi wa jam’iyyar zagon ƙasa, cin zarafin shugabanni wanda ya saɓawa kundin tsarin jam’iyyar.
Waɗanda abin ya shafa dai sun haɗa da
Muhammad Shehu Koko, Mataimakin shugaban jam’iyyar APC Muhammad Danyado, sakataren jam’iyyar APC Malam Biyaminu Muhammad, da kuma Hajiya Talatu Zauro shugabar mata.
Sauran sun haɗa da shugaban matasa da jami’in walwala da jindaɗi.
Wani na kusa da dakataccen ɗan majalisar da bai so bayyana sunansa ba ya bayyanawa wakilinmu da cewa duk da ba shi da hurumin magana amma dai wannan bai rasa nasara da ƙudurin Muhammad Shehu Koko ne na sake tsayawa takarar kujerar ɗan majalisar dattawa a zaɓe mai zuwa saboda waɗansu suna ganin ba za su kai labari ba idan ya tsaya saboda haka suka kitsa wannan.

By ukarofi