
Daga BELLO A. BABAJI
An ga yadda daďaďďiyar jarumar fina-finan Nollywood, Jumoke George ta ke kuka a wani faifan bidiyo da ya karaďe kafafen sadarwa, inda ta ke cewa tsawon shekaru biyar zuwa shida kenan ba ta da gida kuma ba ta da lafiya.
A wani hira ta shirin ‘Biola Bayo Podcast’, jarumar ta ce kasancewar ba ta da gida, a coci ta ke kwana tsawon shekaru 6.
Ta ce, ta gaji da irin rayuwar kaskancin da ta ke fama da shi, wanda a sanadiyyar haka ba ta ga ďanta mai shekaru 41 ba.
Lamarin da ya sa har yaran da ke cikin cocin da take zama, ita ke ďaukar dawainiyarsu tun tsawon shekaru huďu da suka gabata.
Ta kara da cewa, tun watan Janairun 2024 ba ta da lafiya, wanda a dalilin haka ne ta yi wasu gwaje-gwajen lafiya da ya kai ga tana da bukatar N400,000 domin yin gwajin kwakwalwa da zuciya.
Kawo yanzu ta ce, ta karbi aron kuďaďe a hannun mutane da adadinsu ya kai Naira miliyan 2 saboda matsalolin rashin lafiyarta.
Kazalika, ta bada bayanan asusun bakinta ga waďanda ke son taimaka mata kamar haka: Margaret Olajumoke Olatunde
Gtb-
0215498017.
