Abinda ya sa ba za a soke TETFUND ba – Ministan Ilimi

Spread the love

Daga BELLO A.BABAJI

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana Asusun Tallafa wa Ilimin Manyan Makaratu (TETFUND), a matsayin babban ginshikin ci-gaban manyan makarantun Nijeriya, yana mai cewa ba za a soke shi ba daga cikin kudirin gyaran haraji.

Ya bayyana hakan ne a Legas, yayin taron kwana ďaya na ganawa da jagororin makaratun, wanda TETFUND ta shirya, ranar Juma’a.

Ministan ya kawar da fargabar da masu-ruwa-da-tsaki da dama ke yi na tunanin rushe TETFUND, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin kuďi ga asusun wanda daga ciki akwai harajin kaso 50.

Ya ƙara da cewa, kokarin da asusun ke yi wajen inganta manyan makarantu abin a yaba ne da ke bukatar ƙarfafawar gwamnati.

Haka kuma ya gargaɗi makarantun da ba sa sarrafa kudaden TETFUND da suka karɓa yadda suka dace, waɗanda ya ce akwai yiwuwar a cire su daga cikin makarantun da ke cin gajiyar asusun.

Alausa ya ƙara da cewa, yana da muhimmanci a kula da tsarin raba kudaden da sarrafa su ta yadda za a tabbatar yin adalci a kowace gaba.

By Babaji