Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Colin Huang, hamshaƙin attajirin nan na ƙasar Chana kuma mamallakin kasuwar intanet ta Pinduoduo na ƙasa da ƙasa mai suna Temu, ya samu ribar dala biliyan 4.37 a shekarar 2025, wanda ya kai arzikin sa zuwa dala biliyan 38.6.
Wannan ci gaban na nufin ya samu arziki fiye da Aliko Dangote, hamshaƙin attajirin nan na Nijeriya wanda ya mallaki katafaren matatar man fetur ta Dangote kuma hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka da aka kiyasta kuɗinsa ya kai dala biliyan 23.3.
Ci gaban arzikin na Huang ya kuma sanya shi a gaban wasu fitattun attajiran Nujeriya da dama da suka fito cikin jerin masu kuɗi na Forbes na shekarar 2025.
Daga cikin waɗannan manyan ‘yan kasuwan Nijeriya akwai Mike Adenuga, shugaban kamfanin sadarwa na Globacom, wanda a halin yanzu yake riƙe da muƙamin mutum na biyar mafi arziki a nahiyar Afirka da dukiyarsa ta kai dala biliyan 6.8. Haka kuma a cikin jerin sunayen akwai Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, wanda ke matsayi na shida a Afirka da dukiyar sa ta kai biliyan 5.1.
Na ƙarshe a wannan jerin shi ne hamshaƙan attajiran Nijeriya, wato Femi Otedola, shugaban kamfanin da ke riƙe da bankin FirstBank, wanda ya bayyana a matsayin ɗan Nujeriya na huɗu a jerin masu arziki wanda dukiyar sa ta dala biliyan 1.5.
Wanda ya girma kuma taso a Hangzhou, Huang ya nuna basirar sa tun yana ƙaramin yaro ilimi, inda ya halarci makarantar koyon Harshen Waje na Hangzhou yana ɗan shekara 12. Daga baya ya sami digiri daga Jami’ar Zhejiang kuma ya yi digiri na biyu a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Wisconsin.
Huang ya fara nuna ƙwarewar sa ne a hedkwatar Google ta Amurka a cikin 2004, inda ya yi aiki a matsayin injiniyan software da manajan ayyuka. Bayan shekaru biyu, ya koma ƙasar Sin don taimakawa wajen ƙaddamar da Google a Chana.
A shekara ta 2007, ya kafa Ouku.com, gidan sayayya ta yanar gizo, wanda ya sayar a shekarar 2010. Ya ci gaba da Leƙi, dandalin tallata kasuwanci na masu sayar da manyan shafukan yanar gizo na ƙasar Sin, daga baya kuma ya koma harkar wasanni na ‘Game’ a WeChat.
