‘Yan siyasa da jami’an sojoji na daga cikin ƴan tsegumi ga Boko Haram, inji Zulum

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya zargi wasu daga cikin jami’an sojoji da ƴan siyasa da yin tsegumi tare da taimaka wa mayaƙan Boko Haram.

A wata hira da ‘News Central’s Breakfast Central’ a ranar Laraba, gwamnan ya ce “Mu na da masu tsegumi da masu yin zamba-cikin-aminci acikin jami’an sojojin Nijeriya, ƴan siyasa da cikin garuruwan.”

Zulumi ya ci alwashin hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a yi wa ƙoƙarin gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci zagon-ƙasa a jihar.

Ya kuma ce, gwamnatinsa za ta ƙarfafa matakan tsaro na sirri domin magance matsalolin ta’addanci da masu taimaka masa, yana mai alwashin kawo ƙarshen hakan cikin watanni shida.

Ya ƙara da cewa, al’amarin tsaro ba abu ne da ke buķatar a siyasanatar da shi ba, wanda sai an yi nazari game da maslahar al’umma da tattalin arziƙi gabannin samun mafita mai ɗorewa.

Kazalika, Gwamna Zulum ya ce babu yadda za a kawo ƙarshen ayyukan tada ƙayar-baya ta hanyar tuba daga wasu daga cikin ƴan ta’addar, yana mai bada misali da guda sama da 300,000 da suka tuba, waɗanda ya ce ba zai bada lamunin komawar wasu daga cikinsu ba.

Har’ilyau, ya soki rashin kayan aiki daga ɓangaren sojoji da kuma zargin mayaƙan da mallakar makamai masu ƙarfi sama da na sojojin, lamarin da ya ke hana ruwa a yaƙi da ta’addancin.

By Babaji