INEC ta kafa ɓangaren fasahar AI don inganta zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da samar da ofishin fasahar zamani ta AI, wato ‘Artificial Intelligence’ a ķarķashin ɓangaren kula da bayanan na’ura (ICT).

INEC ta sanar da haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinanta na ƙasa kuma Shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu zaɓe, Sam Olumekun, ranar Alhamis.

Ya ce, an yi hakan ne da nufin amfani da ci-gaban da AI ta kawo domin da magance munanan tasirin fasaha a yayin zaɓuka musamman a na shekarar 2027.

Olumekun ya ce, ofishin zai taimaka wa hukumar wajen sarrafa amfani da fasahar tare da waɗanda ake amfani da su wajen gudanar da harkokin zaɓe a ƙarƙashin jagorancin AI.

Ya kuma ce, ci-gaban zai sauķaķe hanyoyin yanke hukunci, kula da harkokin gudanarwa da damawa da masu zaɓe.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, fasahar za ta taimaka wa harkokin ICT a ayyukan hukumar tare da ƙarfafa sahihancin zaɓe da sharhinsa, yana mai cewa mataki ne mai muhimmanci a kawo sauye-sauyen hanyoyin gudanar da zaɓe.

By Babaji