Yadda Boko Haram ke yaɗa farfaganda a Tiktok

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabashin Nijeriya na ƙaruwa – kuma suna amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa ayyukansu da ɗaukar mayaƙa.

Aƙalla mutane 100 ne aka kashe a sabbin hare-haren da aka kai a cikin watan Afrilu kaɗai, kamar yadda Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno, inda nan ne wurin tashe-tashen hankulan da suka ɓarke tun a shekarar 2009, ya ce jihar na ƙara shiga ikon ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

A lokaci guda kuma, ‘yan ta’adda da masu tallata su a TikTok suna yaɗa bidiyo su suna harbin bindiga, jefa gurneti da wasa da tarin tsabar kuɗi.

Sun watsa bidiyo kai tsaye Na wa’azin aƙidu na ƙin jinin ƙasashen yamma a wani salo mai kama da faifan bidiyo da shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar a farkon rikicin shekaru 15 da suka gabata.

ƙungiyoyin masu aikata laifukan da ke kai hare-hare a ƙauyuka da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a yankin arewa maso yammacin ƙasar sun yi amfani da TikTok a baya.

“An fara ne da ‘yan bindiga,” Bulama Bukarti, mataimakin shugaban gidauniyar Bridgeway da ke Teɗas ya rubuta a kan shafin ɗ cewa. “Yanzu, ‘yan Boko Haram suna gudanar da shirye-shirye a TikTok kai tsaye – suna yaɗa farfaganda, suna tabbatar da tashin hankalinsu da kuma barazana ga duk wanda ya kuskura ya yi magana a kansu.”

Wani ɗan Boko Haram ya yi wa Bukarti barazana a wani faifan bidiyo da aka goge a yanzu na TikTok saboda ya yi magana kan ƙungiyar.

Mai magana da yawun TikTok ya ce, yana da wuya a iya ƙididdige adadin asusun da ke da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci da aka kwace.

Yayin da aka sauke wasu daga cikin waɗannan asusu, wasu da dama na ci gaba da aiki, bisa ga asusun da AFP ta gani a lokacin wallafawa.

“ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da abubuwan da ke da alaƙa da waɗannan ƙungiyoyi ba su da gurbi a kan TikTok, kuma muna ɗaukar matakai akan masu tsattsauran ra’ayi a kan dandalinmu ko a waje,” inji mai magana da yawun kamfanin a cikin wata sanarwa ta imel.

Har ila yau, asusun sun buga tsohon faifan na ainihin wanda ya kafa Boko Haram, Mohammed Yusuf, da na Isah Garo Assalafy, wanda aka haramta wa wa’azi a wuraren taruwar jama’a a jihar Neja saboda amfani da munanan kalamai na cin zarafin dimokraɗiyya da wayewar ƙasashen yamma.

Waɗannan asusun akai-akai suna tafiya kai tsaye, suna hulɗa da mabiya, amsa tambayoyi da karɓar kyaututtukan dijital waɗanda za a iya canja su zuwa tsabar kuɗi.

Rikicin ta’addanci a Nijeriya, wanda a tsawon shekaru ya faɗaɗa zuwa ƙungiyar ‘yan adawa, ya kashe fiye da rayuka 40,000 tare da raba wasu mutane miliyan biyu da muhallansu a ƙasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.

Saddiku Muhammad, wanda tsohon ɗan Boko Haram ne, wanda tun a wancan lokaci ya sauya ra’ayi, ya shaida wa jaridar NewsPoint cewa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai na komawa TikTok a wani ɓangare na ayyukan su bayan jami’an tsaro sun daƙile ayyukan su a manhajar sakonni na Telegram.

“Shugabannin ‘yan ƙungiyar sun fahimci cewa don karkato da hankalin matasa, suna buƙatar su yi magana da su a cikin yaren da suka fahimta,” inji Muhammad.

“Daga dukkan alamu, yana samun sakamako. Suna kaiwa ga matasa masu son kuɗi, wanda hakan zai kai ga shiga ƙungiyar.”

By ukarofi